✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wadanda suka kamu da Coronavirus a Najeriya sun zama 89

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta sanar da karin mutum takwas da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya. Wannan ya…

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta sanar da karin mutum takwas da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya.

Wannan ya sa adadin mutanen da zuwa yanzu aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 89.

An samu karin mutane bakwai a jihar Legas, hakan ya sa Legas ke da adadin mutum 59 da suka kamu da cutar a Najeriya kuma su ke da mafi yawan masu cutar a kasar. Sai kuma guda a Jihar Benuwe.

Hakan ya sa adadin mutanen da suka kamu da cutar a Najeriya ya kai 89.

Jerin jihohin Najeriya da cutar Coronavirus ta bulla  da kuma yawan mutanen da cutar ta kama:

Legas- 59

Abuja- 14

Ogun- 3

Enugu- 2

Ekiti- 1

Oyo- 3

Edo- 2

Bauchi- 2

Osun-1

Rivers-1

Benuwe- 1