Da Dumi Dumi

Wadanda suka kamu da COVID-19 sun haura 200

Ministan Lafiya na Najeriya E. Osagie Ehanire ya ce zuwa yanzu an yi wa mutum 3,000 gwaji

Adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus ko COVID-19 a Najeriya ya haura 200.

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta NCDC ce ta sanar da hakan a shafinta Twitter.

“Zuwa karfe 10.30 na daren 3 ga watan Afrilu, akwai mutum 209 da aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Najeriya”.

Adadin ya kai haka ne bayan da aka samu sabbin kamuwa mutum 25: “Goma sha daya a Legas, shida a jihar Osun, uku a Yankin Babban Birnin Tarayya, uku a jihar Edo, biyu a jihar Osun, daya a jihar Ondo, daya kuma a jihar Ondo”.

Hukumar ta NCDC ta kuma ce an samu karin mutum da suka rasu sakamakon kamuwa da cutar a jihar Edo. Hakan ne ya kawo adadin wadanda suka riga mu gidan gaskiya ta wannan hanya zuwa hudu.

ADVERTISEMENT

Wadanda suka warke aka sallame su zuwa yanzu sun kai mutum 25.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya