✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wadanda suka kamu da COVID-19 sun haura 200

Adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus ko COVID-19 a Najeriya ya haura 200. Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta NCDC…

Adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus ko COVID-19 a Najeriya ya haura 200.

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta NCDC ce ta sanar da hakan a shafinta Twitter.

“Zuwa karfe 10.30 na daren 3 ga watan Afrilu, akwai mutum 209 da aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Najeriya”.

Adadin ya kai haka ne bayan da aka samu sabbin kamuwa mutum 25: “Goma sha daya a Legas, shida a jihar Osun, uku a Yankin Babban Birnin Tarayya, uku a jihar Edo, biyu a jihar Osun, daya a jihar Ondo, daya kuma a jihar Ondo”.

Hukumar ta NCDC ta kuma ce an samu karin mutum da suka rasu sakamakon kamuwa da cutar a jihar Edo. Hakan ne ya kawo adadin wadanda suka riga mu gidan gaskiya ta wannan hanya zuwa hudu.

Wadanda suka warke aka sallame su zuwa yanzu sun kai mutum 25.