✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wadanda suka sace Magajin Garin Daura sun samu horo ne a Libya

Babban wanda ake zargi da kitsa sace Magajin Garin Daura Alhaji Musa Umar Uba, ya bayyana cewa wadansu daga cikin tawagarsa har Libya suka je…

Babban wanda ake zargi da kitsa sace Magajin Garin Daura Alhaji Musa Umar Uba, ya bayyana cewa wadansu daga cikin tawagarsa har Libya suka je suka samu horo kan yadda ake sarrafa bindiga da kwance ta da kuma yadda za su mamayi jami’an tsaro su kwace bindiga daga gare su.

Abdullahi Mohammed mai shekara 26, kuma dan asalin Jihar Kano wanda shi ne babban wanda ake zargi a kan sace basaraken da aka gabatar da shi ga manema labarai tare da mutum 12 na tawagarsa da kuma wadansu mutum 27 da ake zargi da aikata miyagun laifuffuka a Abuja, ya ce sun samu nasarar rike basaraken ne na tsawon wata biyu tare da taimakon wadansu mutum biyu daga tawagarsu wadanda suka samu horon sarrafa bindiga na tsawon shekara biyu a kasar Libya.

Ya ce, tare da taimakon wadannan kwararru biyu da suka samu horo na musamman kan yadda ake sarrafa bindiga da kwance bindiga kirar AK 47 cikin kankanen lokaci da yin kwanton-bauna ga jami’an tsaro tare da kwace makamansu na AK 47, ne suka samu damar tsare basaraken na tsawon kwana 60.

Abdullahi Mohammed ya bayyana cewa bayan sun sace basaraken sun nemi fansar Dala miliyan 30 daga iyalansa kafin ’yan sanda su kama su.  Ya ce sun yanke shawarar a biya kudin fansar da Dala ce saboda su samu saukin dauka ba tare da an dago sub a, kuma ya ce sun shirya sace da garkuwa da Magajin Garin Dauran ne tare da taimakon wadansu mutane Daura bisa sa ran su samu makudan kudi tunda basaraken yana da ’ya’ya masu kudi.

Sun ce biyar daga cikin mutum 13 na tawagarsa da suka sanya hannu a sace basaraken sun fito ne daga garin Daura da ke Jihar Katsina, yayin da biyu suka fito daga Jihar Kano, inda suka ajiye basaraken a karshe.

Da yake gabatar da wadanda ake zargi ga manema labarai a Abuja, Kakakin Hedkwatar ’Yan sandan Najeriya, Frank Mba, ya ce ayarin musamman na leken asiri na ofishin Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya (IGP-IRT da STS), suka kama wadanda ake zargin kan yin garkuwa da mutane da fashi da makami da satar shanu da kisan kai da yunkurin kisan kai da mallakar bindigogi ta haramtacciyar hanya inda aka same su da bindigogi kirar AK 47 guda tara da wasu miyagun bindigogi guda shida da harsasai 383 da kayayyakin hada bama-bamai da sauran miyagun kayayyaki.

Mba, ya ce masu garkuwa da mutanen suna samun nasara ce tare da hadin kan wadansu mutanen kauyuka inda ya bukaci kuma a rika tantance mutanen da ake dauka yaran gida kafin a dauke su a aiki.

Ya ce wadansu daga cikin wadanda ake zargin sun fito ne dag Jamhuriyyar Nijar, kuma an aikata barnar ce da hadin gwiwa da miyagun cikin kasa da abokan hadin bakinsu.

Bayan gabatar da su, wani da yake da hannu a sace Magajin Garin Daura kuma surukin Dogarin Shugaban Kasa ya ce: “Sunana Yusuf Dahiru. Mun sace Magajin Garin Daura ne saboda muna son mu yi amfani da shi mu samu kudi tunda yana da ’ya’ya masu dimbin dukiya.”

Ya kara da cewa: “Abin da muka nema daga iyalansa a matsayin kudin fansa shi ne Dala miliyan 30  (kimanin Naira biliyan 10 da miliyan 800), kuma ba mu ci ribar ko kwabo ba’yan sanda suka kama mu.”

“Gaskiyar magana ban san dalilin da suka ce a kama Magajin Garin Daura ba; abin da kawai na sani jagoranmu ya kawo min aikin in yi, sai na nemo wadansu yarana muka tafi Daura muka gudanar da aikin. Muna da mai gidanmu da yake nuna mana abin da za mu yi, kuma ni kwararren mai sata da garkuwa da mutane ne,” inji shi.

Ya ce: “Mu hudu ne muka je gudanar da aikin kuma tare da taimakon daya daga cikin ’yan tawagarmu mai suna Baba Wali wanda dan garin Daura ne, sai muka samu saukin gudanar da aikin, saboda ya san ciki da wajen garin Daura da kuma motsin kowa a garin.”

Game da yadda suka kula da Magajin Garin Dauran ya ce: “Mun kula da shi sosai saboda mun san matsayinsa. Musamman aka mika min shi don haka na tabbatar an ba shi kula ta sarakuna a kwana 60 da ya yi a hannunmu. Ba mu buge shi ba; ba mu wulakanta shi ba ko kadan. Na kula da shi yadda ya kamata tare da ba shi duk abin da yake bukata.”

Wani dan tawagar mai suna Sarfilu Abdu, wanda aka ba shi umarninyin garkuwar ya shaida wa manema labarai cewa ya shiga ta’asar ce bayan an gaya masa za a yi garkuwar ce don a tilasta hukumomin tsaro su sako wasu mambobinsu da suke tsare a hannunsu. Ya ce bai san cewa an yi haka ne don neman kudin fansa ba da bai shiga ba.

Ya ce, “Wata uku da suka gabata wadansu daga cikin mambobin kungiyarmu suntuntube ni suka bukaci in jagorance su zuwa Daura don sace Magajin Garin Daura. Abin da suka shaida min shi ne suna son sace shi ne don yin musaya da mambobinsu wadanda suke tsare don haka na amince na jagoranci aikin. Amman a ji mamaki, saboda bayan sacewar, sai suka fara neman kudin fansa.”

Wani dan tawagar ’yan bindigar wanda ya ce ya kware wajen samar da bindigogi ga tawagar kuma shi ne babban wanda ake kulla yarjejeniya da shi kan biyan fansar ya ce: “Abdullahi Mohammed wanda shi ma mamba ne na tawagar ya gaya min in nemi fansar Dala miliyan 30. Kuma ni ne wanda na yi bidiyon yadda aka yi garkuwar. Ba a ba mu wani kudi ba kafin a kama mu.”

Shi kuwa wanda shi ne mafi karancin shekaru a tawagar mai shekara 19, ya ce yana cikin harkar ce ta hanyar samar da fasahar sadarwa ga masu garkuwa da mutanen wadanda suke tuntubarsa lokaci-lokaci. Ya ce, shi da abokan ta’asarsa sun yi bidiyoyi da dama ga masu garkuwa da mutanen kafina kama su.

Abdullahi Mohammed, ya ce “Wani mai suna Suleiman ne ya sanya ni a harkar garkuwa da mutane, kuma na shiga an dama da ni a garkuwa da mutane sau biyu, inda aka sace wadansu Turawa da ni, kafin abokina Bilal ya jawo ni a garkuwar da aka yi da Magajin Garin Daura.”

Ya ce domin samun kwarewa a harkar garkuwa da mutane ya samu horo a kasar Libya inda aka koyar da shi yadda zai harhada bindiga da wargaza ta da harbi da kisa da kuma yadda za a kwace bindiga daga jami’an tsaro.

Ya ce, ya shafe lokaci yana harkar satar mutane don neman fansa kuma ya samu kudi sosai. “Muna yin bidiyo da kuma tattauna biyan kudin fansa ga tawagar. Kuma saboda ina son in yi fice a harkar na tafi Libya don samun horo a can inda na shafe wata 18. An horar da ni kan yadda ake sarrafa AK 47; kuma an horar da ni kan yadda zan kwace bindiga daga jami’an tsaro da suke dauke da bindiga kirar AK 47 da yadda za mu kwanton bauna. Mun samu horo a Libya, kuma cikin mu 13 da aka kama biyu mun je samun horon, Ibrahim da ni, kuma an tura mu can ne ta hanyar daukar nauyinmu,” inji shi.