✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wadansu na neman tada fitina a Kafanchan

A safiyar Litinin da ta gabata ce aka wayi gari wadansu mutane da ba a san ko su wane ne ba  sun tumbuke sababbin itatuwan…

A safiyar Litinin da ta gabata ce aka wayi gari wadansu mutane da ba a san ko su wane ne ba  sun tumbuke sababbin itatuwan da aka dasa da aka kewaye Babban Masallacin Idi na garin Kafanchan da ke Unguwar Hayin Gada, sannan suka tattara kwandunan da aka kewaye itatuwan suka kone a harabar masallacin.

Wata takarda da aka aike wa Gwamnan Jihar Kaduna da jami’an tsaro da kuma Shugaban Karamar Hukumar Jama’a da sauran masu ruwa-da-tsaki a ranar Talatar da ta gabata dauke da sa hannun Shugaban Kwamitin Masallacin Juma’a da Idi na garin Kafanchan, Alhaji Auwalu Yahaya da Aminiya ta samu kwafi, ta bayyana cewa irin haka ya taba faruwa a shekarar 2013, yayin da aka fara yin katanga don kewaye masallacin inda wadansu da ba a san ko su wane ne ba suka rusa ginin.

“Don haka muke son jawo hankalin hukumomi don yi wa tufkar hanci, domin alamu ne da ke nuna neman tada fitina da wadansu marasa son zaman lafiya ke son haddasawa a yankin. Don haka muke fatan hukuma ta yi amfani da matsayinta don dakile mugun nufin masu son wargaza zaman lafiya a yankin,” takardar.

Masallacin Idin da ke kan hanyar zuwa Makarantar Sakandaren ’Yan mata ta Je-ka-Ka-dawo, yana kan iyaka ne da Masarautar Fantswam. Kuma an ce wadansu dalibai Musulmi ne suka fara ganin wannan barna da safiyar Litinin da ta gabata, lokacin da suke zuwa makaranta abin da ke nuni da cewa hakan ya faru ne ranar Lahadi da dare.

Wani bawan Allah matashi mai suna Isyaka Abdu Ladan ne ya dau nauyin kewaye masallacin da itatuwa, bayan rusa katangar da aka yi yunkurin ginawa shekaru shida da suka gabata, domin kare wurin daga mayar da shi wajen cin kasuwa da kuma tsabtace shi daga kazantar wasu dabbobi da ke zama a ciki, wadanda suka hada da awaki da aladu da karnuka, baya ga samar da inuwa ga masallata da kuma iyakance shi daga gonakin da ke kewaye da shi.