✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wadda aka haifa ba hannuwa ta zama jami’ar Soja

… Tana amfani da kafafunta wajen tuki da amfani da wayar sadarwa da sauransu Wata budurwa ’yar Jihar Florida a kasar Amurka mai suna Donabia…

… Tana amfani da kafafunta wajen tuki da amfani da wayar sadarwa da sauransu

Wata budurwa ’yar Jihar Florida a kasar Amurka mai suna Donabia Walker ’yar shekara 16 da aka haifa babu hannuwa ta kammala samun horon soja ta karamar jami’a (Kadet). An dai haife ta ce tare da larurar rashin hannuwa tun tana cikin mahaifa.

Tun tana karamar yarinya ta fara koyon yadda za ta iya amfani da kafafunta wajen yin wasu ayyukan gida. Kamar amsa kiran wayar sadarwa da tukin mota.

A yanzu da take makarantar Winterhaben ta kasance kwamanda a makarantar horar da Kadet ta ‘Junior Reserbe Officers’ Training Corps (JROTC),’ ta ce, tana fata wadanda suke da nakasa su yi koyi da ita a kan duk abin da suka sa a gaba.

A lokacin da mahaifiyar Donabia, mai suna Tisa Jones take da cikinta likitan da take lura da lafiyarta ba ta bayyana ma ta cewa, ’yar cikinta da za ta haifa, ba ta da hannuwa tun tana cikin mahaifa ba.

Tisa ta ce, “Na ji kamar an yi watsi da ni ce saboda babu wanda ya fada min komai. A tunanina na  dauka wanda ya yi hoton jaririn da zan haifa zai gano cewa, ’yar da zan haifa ba ta da hannuwa.”

Bayan Tisa ta haifi Donabia wacce take dauke da cutar rashin hannuwa. Bincike bai bayyana dalilin faruwar hakan ba, amma an gano cewa, ana iya samun jaririyar da za a haifa da irin wannan cutar a farkon kwana 24 zuwa 36 na lokacin hallita a cikin mahaifar.

Har yanzu dai ba a san adadin mutanen da ke fama da irin wannan larurar ba saboda ta fi kama  jarirai da zarar ta kama su, lokacin kadan bayan haihuwarsu sai su rasu.

A cewar cibiyar lafiya ta kasar, a yanzu ana iya samun masu dauke da irin cutar kashi 50 cikin 100. Wadanda suka hada da cutar za ta iya hana jarirai rufe lebbansu da cutar koda da cutar da take shafar huhu.

Sai aka yi sa’a an haifi Donabia ba tare da irin wadannan cututtuka ba, amma da farko mahaifiyar Donabia ta firgita da yanayin da ta haifi ’yarta.

A kuruciyar Donabia ta kasance tana amfani da kafafunta wajen gudanar da wasu fasahohin na yau da kullum, ta zauna ta gudanar da abin da take so a natse. Hakan ya sa ta koya wa kanta yadda ake tukin mota da kafafunta, tana amfani da kafarta ta dama wajen juya sitiyarin motar da kuma amfani da yatsun kafar hagu wajen amfani da birki.

Donabia ta nuna bajintarta ce lokacin shirin JROTC inda ta jagoranci rundunar da take atisaye daban-daban har da hawa dutse.

Mai ba da umarni a rundunar su Donabia Saje Manjo Rudy Carter, wanda ya yi ritaya daga aikin sojin Amurka ya nuna sha’awar kokarin Donabia lokacin da yake horar da su shekara uku da suka gabata.

A yanzu Donabia na shirin kammala karatunta kuma ta ci jarrabawar tukin mota da sauran gwaje-gwajen da ake yi mata. Donabia ta ce, “Ina son bai wa masu nakasa shawara cewa, duk da irin halin da suke ciki su yarda da kansu kuma su yi hulda da mutanen da za su sake a kan abin da suke da sha’awa.”