✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

WAEC ta kama masu kula da jarabawarta suna magudi

Hukukumar Shirya Jarabawa ta Yammacin Afirka (WAEC) ta kama wasu jami’ai da ke fitar da takardar jarabawar ta bayan fage. Shugaban Ofishin WAEC na Najeriya…

Hukukumar Shirya Jarabawa ta Yammacin Afirka (WAEC) ta kama wasu jami’ai da ke fitar da takardar jarabawar ta bayan fage.

Shugaban Ofishin WAEC na Najeriya Patrick Ehidiamen Areghan ya ce an kama jami’an ne a Jihohin Nasarawa, Ribas da Bauchi, yayin da su ke dab da cika hannu da wasu a Kano.

Ya koka da cewa WAEC ta jima ba ta taba samun matsalar ba sai bana da bata-garin masu kula da jarrabawar suka dauki hotonta suka tura a wasu zaurukan sada zumunta na WhatsApp.

Mista Patrick ya yi bayanin hakan ne a Abuja yayin ran-gadin duba yadda ake kiyaye ka’aidojin kariyar cutar COVID-19 yayin jarrabawar a ranar Laraba.

Ya ce, “Mun tsara takardun tambayoyin yadda ya kamata. Duk wanda ya yada takardar, ko malami ko dalibi za mu kama shi ya yi bayani. A yau (Laraba) ma za mu kama wasu da yawa daga cikinsu.

“Abin da ke faruwa a ’yan kwanakin nan na da ban haushi yadda wadansu mutane da ma’iakatar ilimi ta zaba ta kuma amince da su a matsayin masu kula da jarrabawar suka wallafa ta a intanet.

“Za su dandana kudarsu saboda yanzu muna da fasahar da za bin diddigi mu gano dukkan wanda ya yada ta intanet.

“Yanzu haka na tura sako ga mai kula ofishin shiyyarmu na Kano kan ya ziyarci wasu makarantu don cafko mana wasu daga cikinsu. Ko ka gudu birnin London sai mun cimma ka”, inji shi.

“Na kuma yi magana da Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya kuma mun shirya kawo wadanda ake zargin zuwa Abuja. Za mu bajekolinsu domin mutane su gan su ko ya zama izina ga wasu”, kamar yadda ya ce.

Sai dai jami’in ya ce zuwa yanzu babu cibiyar rubuta jarrabawar da za su rufe har sai an gama fitar da sakamakonta an tabbata ta hanyar kwararn hujjoji cewa makaranta ko cibiyar da ake zargi ta yi magudin jarrabawa.