✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Waiwaye kan darussan baya (6)

Tuna Baya….Wadanda suka saba karanta wannan shafi, tun farkon farawa, sun san cewa a duk karshen zango, mukan zauna don yin waiwaye, abin da Malam…

Tuna Baya….
Wadanda suka saba karanta wannan shafi, tun farkon farawa, sun san cewa a duk karshen zango, mukan zauna don yin waiwaye, abin da Malam Bahaushe ke kira “Adon tafiya.”  A yanzu shekarun wannan shafi namu shida ke nan da watanni shida cif-cif.  Kuma wannan shi ne zama na shida da za mu yi, don yin bitar darussan da muka yi ta kwasa a baya.  
Ga wadanda ba su san wannan tsari da shafin ke gudanuwa a kai ba, shafin Kimiyya da kere-kere ya samo asali ne cikin watan Oktoba na shekarar 2006; farkon taken shafin shi ne: Kimiyya da Fasaha.  Mun kuma yi waiwaye karo na daya, da na biyu, da na uku ne a tsakanin shekarar 2006 zuwa 2008.  Zama na karshe da muka yi, wanda shi ne waiwaye na hudu, ya zo ne cikin watan Satumba na shekarar 2008, daidai lokacin da shafin ya cika shekaru biyu ke nan.  
Ga shi mun sake dawowa a yau don yin nazari kan kasidun baya, a karo na shida, kamar yadda masu karatu za su gani daga taken kasidar.  A yau ma za mu yi nazari ne kan darussan da muka koya a wannan zango.  Zama na karshe mun yi shi ne cikin watan Mayu na shekarar da ta gabata. Bayan haka, za mu ga yawan kasidun da muka kawo a zangon, da abin da suke karantarwa, da irin usulubin da muke bi wajen tafiyar da shafin, da tsarin mu’amala da masu karatu, da kasidun da ba a gama su ba, sannan mu ji inda za mu dosa a zangon da ke tafe.
Me Muka Koya Daga Darussan Baya?
Da farko dai, wannan shafi ya faro ne da kasidu kan fasahar Intanet da sadarwa zalla.  Daga baya ne muka sauya wa shafin take daga: Kimiyya da Fasaha zuwa Kimiyya da kere-kere.  Wannan sauyin take ya samo asali ne sanadiyyar sauyin nau’ukan fannonin da shafin ke magana a kai.  Daga fasahar Intanet da wayar salula zuwa sauran fannonin kimiyya da kere-kere, da sararin samaniya, da sinadarai, da halittar jikin dan Adam, da kuma fannonin dabi’u da zamantakewa.  Ya zuwa makon da ya gabata, mun gabatar da kasidu guda 256 kan dukkan wadancan fannoni.  Idan muka hada da kasidar wannan mako, sun zama 257 ke nan.  A waiwaye adon tafiya na farko muna da kasidu 7.  A zango na biyu muna da kasidu 22.  A zango na uku muna da kasidu 17.  A zango na hudu muna da kasidu 33.  A zango na biyar muna da kasidu guda 132. Sai zango na shida, wanda muke bitarsa a yau ke nan, muna da kasidu guda 46, har da wannan ke nan. Idan ka kebe wannan zango, dukkan kasidun sauran zangunan suna nan daram!  Zan fadi dalilin rashin kammaluwar kasidun wannan zango nan gaba.
Kamar yadda bayani ya gabata a sama, a wannan zango mun gabatar da kasidu kan nau’ukan ilimi daban-daban.  Zangon ya bude ne da kasida kan Mazan Jiya, inda bayani ya zo kan shahararren Malami Ibn Al-Haitham, daya daga cikin manyan malaman Musulunci da suka shahara a fagen ilimin kimiyya a karnonin baya.  
Sai kasida kan samuwar haruffan Hausa masu lankwasa a kwamfutocin zamani, mai taken: Akwai Haruffan Hausa cikin Kwamfutocin Zamani.  Daga nan kuma muka faro shahararriyar silsila kan yadda matasanmu ke gudanar da rayuwarsu a dandalin abota ta Intanet mai suna ‘Facebook’.  Taken kasidar shi ne: Rayuwar Matansamu a Dandalin ‘Facebook’.  Mun kuma gabatar da kasidu biyar a wannan bangare, kuma za mu ci gaba.  
Daga nan kuma sai shafin ya kutsa fagen ilimin kimiyyar sinadaran halitta, wato Molecular Biology, inda muka faro silsila mai take: Tsarin Gadon dabi’u da Siffofin Halitta.  A nan ma mun gabatar da kasidu har shida, za mu kuma ci gaba, in Allah Ya so.  Don har yanzu ko rabin bayanan ba mu kawo ba.  
Daga cikin kasidun wannan zango har wa yau akwai mai taken: Tsarin Mu’amala da Wayar Salula, wanda ci gaba ne cikin jerin kasidun da muke kawowa a wannan fage, da irin ci gaban da ake samu lokaci-lokaci.  Wannan kasida da wannan take ta dauki tsawon makonni 12.  Wannan ya faru ne sanadiyyar tafiya da na yi na kusan watanni biyu a shekarar da ta gabata.  Bayan na dawo kuma sai muka kwashe makonni kamar uku muna amsa tambayoyi, tare da tsokaci ko gyaran da masu karatu suka aiko mana.  
Gama wannan ke da wuya sai ga kasidu hudu a jere, masu taken: Dandatsanci: Sabon Salon Yaki a Tsakanin kasashen Duniya.  Idan mai karatu ya samu karanta wadannan kasidu duka, ba zai yi mamaki kan dambarwar da ke faruwa tsakanin kasar Amurka da wasu kasashe ba cikin wannan mako, kan batun tsohon ma’aikacin hukumar CIA mai suna Snowden.  Idan dambarwar ta ci gaba, watakila mu kawo kasida guda daya don amfanin mai karatu.
Daga nan kuma sai kasida ta musamman kan bacci a mahangar kimiyya, mai taken: Samuwar Bacci da Mafarki a Manhagar Kimiyya.  A wannan fage mun kawo kasidu guda uku ne rak, amma batun bai kare ba.  Domin bayanan sun tsaya ne kan bacci kadai, ba mu tabo batun mafarki ba. Don haka da sauran rina a kaba.  Kada in mance, kungiyar Tsangayar Alheri da ke Dandalin abota ta Intanet ta gayyace ni zuwa babban taronta na shekara-shekara da aka yi a Katsina cikin watan Janairun wannan shekara.  Na kuma halarta, tare da gabatar da kasida daya mai shafuka 11.  Wannan kasida mai take: Rayuwar Matasa a Dandalin Abota ta Intanet, an buga ta a wannan shafi har na tsawon makonni biyu.  
Sai kuma kasida mai take: Ku Inganta Mana Makarantun Kimiyya da kere-kere, wanda muka samu makonni uku muna kawowa, amma Allah bai kaddari mun gama ba.  Sauran kasida guda daya, wacce za ta cike sauran bayanan da suka gabata.  
Wadannan su ne wadanda zan iya kawowa cikin kasidun da suka gabata.
Ina Muka Dosa?
A zangon gaba, in Allah Ya so, akwai ci gaban wasu kasidun, da kuma kawo wasu sababbi, masu tsawo ko matsakaita.  Daga cikin wadanda za mu ci gaba da su akwai Bayani Kan Wayar Salula, wanda ya zuwa yau bayanan sun kai shafuka 83.  Sannan za mu ci gaba da bayanai kan Tsarin Gadon dabi’u da Siffofin Halitta (Genetics), da bayanai kan Rayuwar Matsa a Dandalin ‘Facebook’, sai kuma karashen kasidarmu mai taken: Samuwar Bacci da Mafarki a Kimiyyance, tare da kasidar: Ku Inganta Mana Makarantun Kimiyya da kere-kere.  
A baya ma akwai kasidun da ake bi na bashi, kamar kasidar: Samuwar Ruwa da Sinadaran da ke Cikinta, ba mu karasa ta ba; da kuma kasida mai taken: Makamashi da Dukkan Nau’ukansa, shi ma ba mu gama shi ba.
Bayan wadannan, in Allah Ya so akwai sababbin kasidu a fannin kere-kere.  Za mu kawo bayanai kan tasirin kimiyyar fasahar bayanai ga fannin kere-kere.  Wannan kasida za ta dubi yadda fannin kera motoci a duniya ke amfani da masarrafan kwamfuta wajen inganta hajojinsa.  Sannan za mu kawo bayanai na musamman kan babban titin dogo na zamani da ke birnin Dubai, watau Dubai Metro Train Track; yadda aka gina shi, da tsarin kirar jiragen, da makamashin da suke amfani da shi wajen dibar jama’a daga zango zuwa zango.  Dadi na nesa, wai Ungulu ta hango (leka) masai. Sai kuma bincike kan tasirin kimiyyar sadarwa ga zamantakewar jama’a a duniya baki d,aya.
Mu’amala da Masu Karatu
A wannan zango ma kamar sauran zangunan da suka gabata, masu karatu sun rubuto tambayoyi, wasu na amsa su nan take, wasu kuma na buga su, wasu kuma, wadanda maimaitattu ne, ban saurare su ba.  Sannan akwai wadanda suka bugo waya don nuna gamsuwa, ko don godiya ko kuma neman karin bayani kan kasidar da suka karanta a makon, nakan saurare su, duk da cewa na ce ba a kira, sai dai a rubuto tes.  dan Adam ajizi ne.  Akwai kuma wadanda suka rubuto don bukatar kasidun baya, su ma nakan aika musu.  Wasu in aika musu nan take, wasu kuma sai bayan wani lokaci. Ya dai danganci halin da na samu kaina sadda suka aiko bukatarsu.
Har wa yau a cikin wannan zango na samu sakonnin gyara sosai daga wajen masu karatu.  Shahararre daga cikinsu shi ne wanda na samu daga Malam Auwal Yakubu, wani masanin fannin kimiyyar sararin samaniya.  Na kuma buga a wannan shafi, ina kuma mika godiyata a gare shi matuka. Allah saka masa da alheri.
Za mu cigaba