✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wajibcin girmama Makka da Madina ga mahajjata (1)

Fassara Abubakar Hamza Ya ku Musulmi! Wadannan matafiya mahajjata ne suka kusanto, suna keta sahara mai halakarwa, sun kutso falalen kasa da kilomitoci. Sun jigata…

Fassara Abubakar Hamza

Ya ku Musulmi! Wadannan matafiya mahajjata ne suka kusanto, suna keta sahara mai halakarwa, sun kutso falalen kasa da kilomitoci. Sun jigata a cikin tafiyarsu, sannan sun zo bi-da-bi, ayari na biye da ayari a cikin sahara da sararin samaniya.

Ya fatana! Shin zan tashi in wayi gari sai in sunsuni ciyawar Izkhiri ta Makka da karan shukinta (na Jalil).

Sai kuma in kwance jakata a kasar Annabi (SAW) domin in kwana a Harami Madaukaki ina bako. Sau da yawa, yawale mai yawo da tafiye-tafiye, yanki-yanki, kasa-kasa, birni-birni, mai yawaita bulaguro, wanda yake karar da taro da sisinsa a kan haka. Sai ka samu, ya yi nawa da sakaci kan tafiyar sauke ibadar Hajji, ba tare da uzuri ba, na tsawon shekaru, har ya tsufa.

Ba ya burge zuciyata, sautin karamin tsuntsu mai rera waka, haka kuma murmushin fikar karamin yaro a lokacin bulaguro!

Saboda ba kowane balaguro ke kayatar da ni ba. Sai dai balaguro zuwa ga Hajji wanda za a saka mana da Aljanna. Wannan kuma baiwa ce daga kyautar Allah Makadaici

Ya ku Musulmi! Makka da Madina garuruwa biyu masu haske da tsarkaka, su ne wurare biyu da suka fi sauran garuruwa daraja mudlakan, kuma su ne suka fi kowane bigire a doron kasa girman matsayi bisa ijma’in malamai.

Saboda Makka nan ne wurin da wahayi ya fara sauka, mabubbugar addini, gari amintacce, alkiblar Musulmi, makarkata ga zukatan muminai, uwar alkaryoyi, wadda ba ta da makamanci a cikin birane, kuma ba ta da tsara a cikin kasashe.

Ita kuma Madina, ita ce gari abin so ga masoyinmu (SAW), ita ce gidansa matabbatarsa, kuma garin da ya yi hijirarsa ta farko, garin Sunnah, mafakar imani kuma ganuwar imani mai ba shi kariya, kuma mafakar Musulunci da Musulmi.

Wahayi bai sauka ba, face a kasar Makka da Madina, kuma fitilar Manzanci ba ta haska ba sai a kan kasarsu, kuma Annabi (SAW) bai rayu ba face a kan turbayarsu.

An ruwaito daga Abdullahi dan Abbas (Allah Ya kara yarda a gare su), ya ce:

“Manzon Allah  (Sallallahu Alaihi Wasallam)- a ranar da aka je Yakin Bude Makka, ya ce: “Lallai Allah Ya haramta wannan gari (Makka), a ranar da Ya halicci sammai da kasa, don haka; Makka Harami ne da haramtawar Allah, har zuwa Ranar Kiyama. Kuma lallai yaki a cikinta bai halatta ga wani mutum a gabanina ba, kuma ni ma bai halatta a gare ni ba, sai a cikin wani zangon lokaci na yini. Kuma lallai Makka Harami ne da haramtawar Allah, har zuwa Tashin Kiyama; ba a yanke kayar Harami, ba a korar abin farautar Harami, ba a daukar abin tsintuwar Harami, sai ga wanda zai ba da cikiyarsa, ba a cirar ciyawar da ta tsira a cikinsa.”

Sai Abbas (RA) ya ce: “Sai dai ciyawar Izkhir, saboda amfanin makeransu da bukkokinsu?”

Annabi (SAW) ya ce: “Sai dai ciyawar Izkhir.” (Buhari 1834, 3189) da (Muslim 1353), suka ruwaito shi.

Kuma Manzon Allah (SAW) ya mayar da Madina Harami, kamar yadda annabi Ibrahim (AS) ya mayar da Makkah Harami, kuma ya karkata zuwa ga Madina sai ya ce: “Lallai Madina Harami ne amintacce.”

Don haka, idan ganyen bishiyar Harami da abin farautar Harami suka kasance masu alfarma ababen girmamawa, to yaya alfarmar Musulmi da alfarmar Hajji da kuma alfarmar mahajjata da amincinsu da ayyukansu na Hajji za su kasance?

Don haka ba ya halatta Musulmi ya haifar da abin da zai kawo tasgaro ga amincin gari Mai alfarma, ko tasgaro ga tsarin garin da natsuwarsa da walwalar wadanda suka nufo Makka da mazauna cikinsa, kuma bai halatta Musulmi ya cutar da Musulmi da zancensa ko aikinsa ba.

Allah Ta’ala Ya ce: “Kuma wanda ya yi nufin ilhadi (karkatar da gaskiya) a cikinsa (Makka) da zalunci, za Mu dandana masa wata azaba mai radadi.” (Hajji: 25).

Don haka, idan niyyar zalunci da yin kudurin ilhadi ko karkatar da gaskiya yana hukunta ukuba mai radadi, to yaya kuma ga mutumin da ya yi ta’addancin aikata laifi mai haddi, ko ya aikata mummunan zunubi, ko ya zubar da jini (kisa), ko ya firgitar da amintattu, ko ya cutar da mai rauni, ko ya zalunci miskini, ko ya cuci mahajjaci; ta hanyar gurbata akidarsa, ko ha’intar alkawarinsa ko cin amanarsa? To mene ne zai kasance sakamako da ukubarsa a wurin Allah, alhalin kuma ya keta alfarmar lokaci da wuri da mutum?

Dana, kada ka yi zalunci a Makkah; kankane ko babba. Ka kiyaye alfarmominta -Ya kai dana! Kada mai rudi ya rude ka.

Dana, lallai wanda ya yi zalunci a Makka zai hadu da sharrori masu yawa.

Domin za a bugi fuskarsa, kuma za a tuntsura shi a Wutar Sa’ira a kan kumatunsa.

Dana, lallai ni na jarraba hakan, sai na samu mai yin zalunci a Makka yana yin hasara Allah ne Ya yi mata baiwar aminci da abin da aka gina a cikinta na benaye.

Kuma Allah Ya amintar da tsuntsayen cikinta, domin tsuntsu ba ya da tsoro a Makkah.

Giwaye, an halakar da rundunarsu ana jifansu a garin da duwatsu.

Sai ka ji, idan ana ba ka labari, kuma ka fahimci yaya karshen al’amura suke kasancewa.

Yana shiga ma’anar zalunci da ilhadi a Masallacin Harami: Aikata laifuffukan haram a Makka, ko neman halatta su, kamar bayyanar da shirka da bidi’o’i da aukawa cikin zina da shan giya da sace-sace da cinye dukiyoyi da makirci da wayo, da daga tutoci domin raya bangaranci da bidi’o’i da alamomin shirka da shuka fitina da rura wutar sabani da haifar da bambance-bambance a tsakanin mahajjata da daukar taron Hajji a matsayin wurin yada jita-jita na karya da lalatattun akidu, ko yada sabubban kiyayya da adawa, saboda wasu manufofi na siyasa, ko kabilanci ko bangaranci ko akida ko mazhaba.

Kuma Hajji da wadannan wuraren masu tsarki, lallai suna da girma da tsarkin da suka fi karfin a mayar da su wuraren yada wadannan ayyukan masu muni. Kuma al’amarin Hajji da amincinsa yana ga hannaye masu karfi, masu ginawa, masu ba da kariya, masu tausayi, wadanda ba za su bar miyagun mutane da suke nufin gurbata lafiyar Hajji ko siyasantar da shi ba. Domin shugabannin za su hana miyagun cimma manufarsu ko kaiwa ga samun burinsu.

Ya ku Musulmi Wajibi ne a kan mutanen Makka da Madina da masu zama a cikinsu da sauran mahajjata da masu Umara da ziyara, su rika girmama wadannan wuraren masu tsarki, su kiyaye su ba su kariya, suna tsarkake su daga ayyukan sabo da munanan laifuffuka ababen ki masu halakarwa.

Mummunan aikin da aka yi a Harami ba a ninka shi ta fuskar adadi, sai dai ya fi girman laifi, kuma ya fi tsananin zunubi, a kan laifin da aka yi a wurin da ba Harami ba.

Ibn Kayyim (Allah Ya yi masa rahama), ya ce: “Yin mummunan laifi a Harami da kasar Harami (Makka) da kuma a kan shimfidar Allah (Masallaci) ya fi girman muni a kan aikata laifi a wani bangare na duniya.”

Kuma ya ce, a cikin littafin Madalibu Ulin nuha: “Kuma ana ninka kyawawan ayyuka da munana idan aka yi su a wuri mai daraja, kamar Makka da Madina da Baitul Makdis da kuma a cikin masallatai. Haka kuma idan aka yi su a wani zamani mai falala, kamar ranar Juma’a da watanni hudu masu alfarma da kuma a kwanakin watan azumi.”

 

Wajibcin girmama Makka da Madina ga mahajjata (2)

Shehun Malami Mar’iy bn Yusuf Alkarmiy ya ce: “Lallai an sani daga shari’a mai haske da addini mikakke, cewa zunubi yana ninkuwa a wurare masu daraja da halaye madaukaka, to haka lamarin yake a wurare masu daraja.” Sa’annan ya ce: Kowane wuri, ko zamani wanda ya fi daraja, to sabon Allah a cikinsa ya fi muni, domin bakar tawada ta fi bayyana ga farin abu.”

Imam Annawawi (Allah Ya yi masa rahama), ya ce: “Zababbiyar magana ita ce, lallai yin makwabtaka da Dakin Allah da kuma Masallacin Manzon Allah a Makkah da Madina mustahabbi ne, sai ga wanda zato ya rinjaya masa cewa, zai auka cikin lamura ababen zargi, ko sashensu. Kuma hakika halittun da ba za a kididdige su ba, daga magabatan al’umma da wanda suke a bayansu, daga cikin wadanda ake koyi da su, sun aikata mujawara  (makwabtaka a Makka da Madina).”

Kuma Kurdabi (Allah Ya yi masa rahama), ya ce: “Haka kuma, shari’a a wurare dayawa ta bayyana cewa, lallai duk lokacin da alfarma ta ninku, sai aka keta su, to ukubar itama sai ta ninku.”

Kuma Shehul Islam Ibnu Taimiyya (Allah Ya yi masa rahama), ya ce: “Yin sabo a kwanakin da ake girmamawa da wuraren da ake girmamawa, zunubinsu da ukubarsu yana yin kauri, gwargwadon falalar zamanin da .wurin.”

Kuma Kurdabi (Allah Ta’alah Ya yi masa rahama), ya ce: “Kuma idan Allah Madaukaki Ya girmama abu, ta bangare guda, to sai ya zama yana da alfarma guda daya, idan kuma ya girmama shi ta bangarori biyu, ko bangarori da yawa, sai alfarmarsa ta kasance mai yawa, to sai a ninninka ukuba a kansa idan aka yi mummunan aiki, kamar yadda ake ninka lada idan aka yi aiki kyakkyawa; domin wanda ya yi biyayya ga Allah a cikin wata Mai alfarma, a kuma gari Mai alfarma, to ladansa ba kamar na mutumin da ya yi masa biyayya a watannin da ba su da alfarma, ko a garin da ba Harami ba. Haka wanda ya masa biyayya a watan da ba ya da alfarma, amma a gari Mai alfarma, ba ya zama daidai da wanda ya yi maSa biyayya a watan da ba ya da alfarma, a kuma garin da ba ya da alfarma.”

Ya ku  Musulmi! Ku girmama ababen da Allah Ya ba su alfarma a cikin halin haramarku da wajensa, kada kuma ku ketare iyakokinSa, kada ku halatta wurare masu alfarma, Allah Ta’ala Ya ce: “Wannan kuma, saboda wanda ya girmama hukunce-hukuncen Allah , to shi ne mafifici a gare shi a wurin UbangijinSa.” (Hajji:30).

Alfarmomin kuma su ne: Girmama Mash’arul Haram (wuraren Hajji) da Daki Mai alfarma da Masallaci Mai alfarma da Gari Mai alfarma, wadannan su ne alfarmomin.

Kuma ku girmama abin da Allah Ya umurce ku da girmama shi, kuma ku gabatar da abin da Allah Ya umarci ku gabatar, kuma ku nisanci abin da Allah Ya hukunta haramcinsa, don ku samu falalarSa da ladarSa da ni’imarSa.

Ina fadan abin da kuke ji, ina neman gafarar Allah, sai ku nemi gafararSa, lallai Shi Ya kasance ga masu mayar da lamuransu gare Shi Mai yawan gafara ne.

 

Huduba ta Biyu

Ya ku Musulmi! Sunnah ta tabbata kan ninka ladar Sallah a Masallaci Mai alfarma da Masallacin Annabi (SAW), wato ninkawa ta fuskar adadi ga farilla da nafila bisa maganar da ta fi inganci daga cikin maganganun malamai biyu.

An ruwaito daga Jabir  (Allah Ya kara yarda a gare shi) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallama) ya ce: “Yin Sallah a Masallacina wannan ya fi salloli dubu a waninsa falala; in ban da Masallaci Mai alfarma. Sallah kuma a Masallaci Mai alfarma ya fi salloli dubu dari, a masallacin da ba shi ba.” Ahmad ya ruwaito shi, (14694 da 15271) da Ibn Majah.

Sai dai babu wani dalili ingantacce da ya nuna cewa, kyakkyawan aikin da aka aiwatar a garin Makka ana ninka ladarsa zuwa lada dubu dari. Ko yake cewa ana ninka ladar azumin Ramadan idan aka yi shi a garin Makka ko a Madina zuwa ladar azumin wata dubu dari, ko a ba da ladar Ramadan guda saba’in. Dukkan wadannan babu Sunnar da ta tabbatar da su, kuma babu wani dalili a kan haka. Kuma hadisan da suke dauke da wannan ma’anar ko dai da’ifai ne, ko yasassun hadisai na karya.

Magana ingantacciya ita ce, lallai kyawawan ayyukan da aka yi a lokaci mai daraja da wuri mai daraja ana ninka ladarsu, ninkawa ta fuskar girma, ba ta fuskar adadi ba, sai abin da dalili (ingantacce) ya yi nuni a kansa.

Kuma su ma munanan ayyukan da aka zartar da su a wurare ko lokutai masu daraja zunubinsu yana bunkasa ta fuskar girma, ba ninkuwa ta fuskar adadi ba.

Ya ku mahajjata da masu Umara da ziyara! Ku ribaci lokacin zamanku a garin Makka da Madina, ta hanyar kwazo wajen aikata kyawawan ayyuka da yawaita aikata su, kuma ku yawaita tuba da neman gafara, kuma ku bayyanar da rusunawarku da kankan-da-kai da nadama da nuna bukatuwarku ga Ubangijnku da bayyanar da lalura; domin kuna wurin saukowar rahama, kuma wuraren karbar ayyuka da fagagen da ake zaton amsa addu’o’i da gafara da ’yanta bayi daga fadawa cikin wuta. Ku rika tuna girman wuraren da falalar lokatan.

Allah Ya hada addu’o’inku da amsawa, neman gafararku kuma da yarda, ayyukan da kuke yi kuma Ya karba.

Sheikh Salah bn Muhammadu Albudair ya gabatar da wannan Huduba ce a ranar Juma’ar da ta gabata (16 ga Zul-Kida, 1440 BH, daidai da 19 ga Yuli, 2019 Mildaiyya. Kuma mun samo ta ce daga shafin fecbook na Ustaz Aliyu Sa’id Gamawa