✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wakilan Shaidan A Watan Ramadan

Ba wannan ne karo na farko ba, amma wannan ne karo na farko da abun yake dawo min a tunani na, yanda nake kallon lamarin…

Ba wannan ne karo na farko ba, amma wannan ne karo na farko da abun yake dawo min a tunani na, yanda nake kallon lamarin tun daga farkon wannan wata mai daraja.

Da ni, da kai da mu da ke, da su, duka iya wadanda ke kallon gabas domin yin Sallah da salati, mun dade tun tasowar mu da sanin wani Hadisi; wanda ko dai muka koya a Islamiyya ko kuma muka jiyo a bakin Malamai kan cewar, duk lokacin da azumin watan Ramadan ya kama, ana bude kofofin Aljanna, a kuma rufe ta wuta sannan ana daure aljanu da shaidanu.

Hikimar hakan, abu ne da sanin sa ya darsu a tunanin kowane mumini mai imani. Wata ne mai daraja, mai falala, watan azumi, watan Sallah da nafila. Wata ne da zamu kira da watan garabasa mai kunshe da kwanaki da lokuta masu ddimbin alfanun da ake farautar gwaggwabar ladar neman kusanci ga Allah buwayi, bisa doron ladubban siffanta kai da kyawawan ayyuka a duk kan janibin rayuwar mu ta yau da kullum.

Haka nan wata ne dake da wa’adin farawa da karewa, wannan tasa duk kan abun da zaka yi a cikin sa (na ibada) ladan sa kan ninku sabanin in ba watan bane. Mai Azumi ana Son ya cusawa kan sa (ko da ba haka yake ba kamin azumin) halaye da dabi’u nagari, tare da yin hannun riga dama nisantar duk wani abu da yake yi na akasin hakan.

Kalmar musulunci akan duk wani abun halitta ita kadai, ba zata zamo masa tsanin kai wa ga rahamar Allah ba, sai ya zama mai bi da kuma kare dokokin Allah cikin duk wani fasali na umurni da kuma hani da aka yi masa cikin ka’idojin shari’ar addinin musuluncin da yake amsa sunan dan cikin sa.

Ba karamin takadiranci, shedanci, tsageranci da kuma rasar kunya bane mutum, ya kasance da wani hali na banza matuka, a boye kuma ya fito sarari yana bayyanar dashi ba, sai dai in dama imani ya kauracewa kokon zuciyar sa.

An kama shaidanu da Aljanu an daure, amma mu kuma gamu da wakilan su a cikin al’ummar mu ta yau. Sun zama jakadun su, suna nan a cikin gidajen mu, makotan mu, unguwan nin mu dama yankin mu gaba daya. Wanda ya daure aljanu da shaidanun nan fa ba shi zai sauko ya daure mana su ba. (Miyagun Mata).

Manzon Allah (S.A.W.) Ya yi gaskiya, a ma’anar wani hadisi, cikin ruwayoyin Bukhari da Muslim, ya bayyana cewa, bai bar wata fitina ba ga maza, bayan shi, face Mata.

Wallahi iyaye ya kamata muji tsoron Allah. Ke Hajiya Wance da Mallam Wane, wadannan ‘ya ‘ya matan da kake da iko akan su, idan har sun daina ci da sha, sun lazimci yin Sallah lokuta 5 din nan, wannan hakkin Allah ne a kan su kai-tsaye. Ku kuma da suke fita a gaban ku, kuke zaune dasu a gida guda, hakkin Allah ne a kan ku, ku lura da irin yanayin shigar da suke yi. Duk lokacin da kaga’yar musulma a titi da shiga mai tayar da hankalin nan, kar ka fara kawo komai sai sakacin iyaye. Damar da ku (iyaye) ke baiwa ‘ya ‘yan ku (mata) na yin shigar da duk suka ga dama a matsayin su na ‘yan mata ne ko zawarawa, bisa manufar ita kadaice hanyar da namiji zai gan su ya kyasa, ita ce mafarin kofar halakar da kuke bude musu. Har ta kai ga yin abun da kuke bin son zukatan ku, har zuwa kan abun da bakwa so kuma baku yi tsammani za’ayi ba.

Nasiha ta gare ku (Iyaye) anan ita ce, ba Sallah da Salati da tsayuwar dare da nafilfili da sadaka gami da ciyarwa kadai ya kamata ku takaita ba, ku fadada wajen kula da tarbiya ta hanyar kame ‘ya ‘yan ku mata ku daure (hana su shigar banza), kamar yadda aka daure shaidanun mutanen boye, don kaucewa barin ‘ya ‘yan ku su kasance jakadun Iblis a ban kasa cikin wannan wata mai albarka.

Ahmad A. Umar 0806038135