✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wanda ya daki matarsa ta mutu ya shiga hannu

Wani magidanci mai shekara 28 da ya yi ta jibgar matarsa har ta mutu ya shiga hannun ’yan sandan a Jihar Ogun, bayan ya yi…

Wani magidanci mai shekara 28 da ya yi ta jibgar matarsa har ta mutu ya shiga hannun ’yan sandan a Jihar Ogun, bayan ya yi wasan buya da su na tsawon mako uku amma dabara ta kare masa ’yan sandan suka yi masa kofar rago, suka kama shi a ranar Litinin da ta gabata a wani gida a yankin Itori a Abeokuta babban birnin Jihar Ogun.

Kakakin  Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi, ya shaida wa Aminiya cewa a ranar 23 ga Satumba ne wanda ake zargin mai suna Kazim Yusuf, ya shigar da bayanai a ofishin ’yan sanda da ke yankin Enugada inda ya ce, matarsa ta yanke jiki ta fadi lokacin da take debo ruwa, “Hakan ne ya sanya jami’anmu suka bi shi zuwa gidan domin bibiyar hakikanin abin da ya yi sanadiyar mutuwar matar mai shekara 26 wacce ta haifa masa ’ya guda, inda jami’anmu suka ga alamun duka a jikin gawarta. Kuma nan take suka gane ba haka ta yanke jiki ta fadi ta mutu ba ba kamar yadda mijinta ya bayyana. Kuma ana tsakiyar bincike sai ya sulale ya gudu,” inji shi.

Ya ce amma jami’ansu sun yi nasarar kama shi bayan mako uku yana buya, ya kuma tabbatar da cewa ta rasu ne sakamakon dukan da ya yi mata  bayan sabanin ya shiga tsakaninsu, inda ya ce a baya ma yana dukanta amma bai taba sanin haka zai yi sanadiyar mutuwarta ba.

Tuni ’yan uwar matar suka yi jana’izarta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada inda ake ci gaba da bincikar wanda ake zargin kafin ya gurfana a gaban kotu domin ya fuskanci hukunci.