✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wanda ya yi yunkurin damfarar Kwamishinan ‘yan sanda ya shiga hannu

Dubun wani dan danfara da ya yi yunkurin danfarar Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogun Bashir Makama, ya cika bayan da rundunar ‘yan sandan jihar suka…

Dubun wani dan danfara da ya yi yunkurin danfarar Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogun Bashir Makama, ya cika bayan da rundunar ‘yan sandan jihar suka yi masa kofar rago.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi ya shaidawa Aminiya cewa, dan danfarar mai suna Tayo Ogunmola mai kimanin shekaru 52 ya kira lambar wayar kwamishinan ‘yan sandan jihar ne inda ya shaida masa cewa ya turo masa lambobin katin waya cikin rashin sani don haka kwamishinan ‘yan sandan ya taimaka ya mayar masa da katin, “daga nan kuma sai ya nemi kwamishinan ‘yan sandan ya ba shi kudi zai taimaka masa domin shi mataimakin babban sufeton ‘yan sandan Najeriya ne, a daidai lokacin da yake wannan maganganun bai san da Kwamishinan ‘yan sanda yake magana ba, inda nan da nan kwamishinan ‘yan sandan ya yi masa kofar rago cikin lokacin kankani ya sanya jami’an rundunar na musanmman masu bin kwakwaf suka kamo dan danfarar a maboyarsa da ke a yankin Araromi” inji shi.