✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani abu kan Masarautar Pindiga

Pindiga, ita ce helikwatar mulkin masarautar Pindiga, wacce kuma ɗaya ce daga cikin masarautun Jihar Gombe. Wannan gari mai daɗaɗɗen tarihi, Jukunawa suka kafa shi…

Pindiga, ita ce helikwatar mulkin masarautar Pindiga, wacce kuma ɗaya ce daga cikin masarautun Jihar Gombe. Wannan gari mai daɗaɗɗen tarihi, Jukunawa suka kafa shi a tsakanin ƙarni na goma sha shida zuwa ƙarni na goma sha bakwai. Garin ya fara daga ɗanƙaramin matsugunni na wasu jama’a a kan dutse har zuwa bunƙasarsa kamar yadda yake a yau a matsayin masarautar sarkin yanka mai daraja ta biyu a cikin Jihar Gombe.

Asali

Pindiga, gari ne mai tsohon tarihi, asalin kafuwar garin ya faro ne daga lokacin da al’ummar Jukunawa suka shigo yankunan baƙaƙen fata daga ƙasar Yamen a ƙarni na 16 zuwa na 17.

Fitowar wadannan jama’a daga Yamen, su shigo ƙasashen bakaken fata, da suka faro daga Sudan ta yau, sai suka yada zango a garin Khartoum. Daga nan suka rankayo ta gefen Kogin Chadi, kama-kama har suka zo Dutsin Bima. Daga wannan dutsi na Bima ne suka rabu gida biyu; kashi ɗaya daga ciki suka kama hanya tiryan-tiryan har zuwa Dutsen Binga, inda suka kafa wani gari wanda a yau ake kira da sunan Yalwa.

A 1815 Miladiyya, Sarkin Gombe Buba Yero, ya fara kai harin yaƙi ga wannan gari na Binga. Dukkan yaƙuƙuwan da wannan Sarki ya yi da Jukunawan Binga, bai samu nasarar murƙushe su ba, har ya bar duniya. Haka nan aka ci gaba da wannan yaƙi har zuwa zamanin Sarkin Gombe Umaru Kwairanga, wanda ya haɗa rundunar haɗaka da ta tattaro mayaƙa daga ƙasashen Bauchi da Misau da Jama’are da kuma wasu garuruwan. Wannan runduna ita ta yaƙi Jukunawan da ke wannan gari na Binga; yaƙi irin na ƙare-dangi, ba ta bar kowa ba sai waɗanda suka gudu suka sha da ƙyar.

Ragowar mutanen da suka famtsama uwa-duniya, su ne suka sake dawowa daga baya suka kafa wani garin a kan wani dutse da suka kira shi da suna ‘Kartum’. Sun zaɓi su kira shi da wannan suna ne don ya riƙa tuna musu da zaman da suka taɓa yi a garin Khartoum da ke cikin ƙasar Sudan ta yau.

Bayan wani lokaci suna zaune a kan dutsen na Kartum, sai suka ga cewa ya kamata su ƙara gaba, saboda haka sai suka gusa gaba kaɗan, tazarar da ba ta haura kilomita ɗaya da rabi ba, suka sake kafa wani sabon gari a kan Dutsen Puli, wanda yanzu ake kira da Dutsen Jukun. Wannan dutse yana nan a bayan garin Pindiga.

Bayan Turawa sun ci Gombe da yaƙi, a 1903, sai suka sauko da waɗannan mutane daga kan wannan dutse zuwa matsugunin da a yanzu suke zaune a ciki; wato garin Pindiga.

Masarauta

Tun daga farko, a lokacin da hedikwatar mulkin wannan yanki na Pindiga ke zaune a matsugunninsa na farko; garin Binga, ikonta ya malala har zuwa garin Gwana daga Kudu maso Gabas zuwa garuruwan Kwami da Gadam. Sai kuma ta ɓangaren Yamma inda ta dangana da garuruwan Fali da Kirfi a Jihar Bauchi ta yau. Da ta miƙe Gabas  ɗoɗar, sai da ta kai garin Gwani, sannan ta karkata zuwa Gabas maso Kudu inda ta kai har zuwa garuruwan Tangale da Wurkum. Alaƙar da ke tsakanin Jukunawan Binga da waɗannan garuruwa da aka lissafa, alaƙa ce ta addini. Ana kuma iya tantance haka daga ɗan sauran tasirin abin da ya rage na al’adu da addini daga Bolewa da Terawa da Waja da Wurkum da kuma Tangale.

Wannan tasiri na wannan gari na Jukunawa wato Binga, ya fara dusashewa a1830 zuwa 1840 inda ta koma ƙarƙashin mulkin Masarautar Gombe a ƙarƙashin tutar Musulunci. An ce, wannan ya faru ne sakamakon karɓo tuta da ɗaya daga cikin ’ya’yan sarautar gidan ya yi mai suna Hassan daga Gombe. Bayan ya karɓi tutar, sai ya koma gida da nufin yaƙar ɗan uwansa mai suna Giwa wanda a lokacin shi ke sarautar ƙasar, sai shi Giwa ya ce ba zai yi yaƙi da ɗan uwansa ba. Saboda haka sai ya ƙara gaba ya kafa garin Tudun Ƙwaya wacce a yanzu take cikin Karamar Hukumar Ɓilliri da Kaltungo a Jihar Gombe. Wannan kuma ya biyo bayan karɓar Musulunci da shi Hassan ya yi, shi kuma Sarki Giwa a nasa ɓangaren ya ƙi karɓar addinin Musulunci.

A farkon ƙarni na 20 kuma; wato a 1903, lokacin da Turawa suka ci ƙasar Gombe da yaƙi, wannan ƙasa ta Pindiga ta koma ƙarƙashin mulkin Hakimin Akko a matsayin garin Dagaci. Tun daga wannan lokaci, Pindiga take a matsayin garin Dagaci har zuwa 1978, inda ta samu ci gaban da ya kai ta matsayin Hakimi a zamanin Sarki Alhaji Ahmadu Shu’aibu.

A cikin shekarar 2000, zamanin Alhaji Abubakar Habu Hashidu, Gwamnan farar hula na farko a Jihar Gombe, Allah Ya albarkaci wannan gari na Pindiga da komawa masarauta mai daraja ta biyu ƙarƙashin Sarkin yanka Alhaji Mohammad Seyoji Ahmad wanda ya zamar mata Sarki na farko.

Ke nan a taƙaice, garin Pindiga, gari ne da Jukunawa suka kafa shi a ƙarni na 16 zuwa 17. Kuma wannan gari ya fara ne daga matsugunninsa na farko mai suna Binga wanda yanzu ake kiransa da Yelwa, sannan bayan yaƙi ya fatattaka garin aka sake kafa wani a kan Dutsen Kartum, sai kuma aka sake matsawa gaba aka sake kafa wani da aka kira da Puli, wanda yanzu kuma ake kiransa da Dutsen Jukunawa, sannan aka gangaro ƙasa aka kafa wannan gari na Pindiga wanda ya zama hedkwatar mulkin masarautar Pindiga, wacce aka samar da ita a zamanin mulkin Gwamnan farar hula na farko Alhaji Abubakar Habu Hashidu a shekarar 2000, wacce kuma Sarkin yanka mai daraja ta biyu, Alhaji Muhammad Seyoji Ahmad ya zama Sarki na farko kuma har yanzu yake a kan kujerar sarauta.

An ciri wani sashi na tarihin wannan masarauta ce daga cikin littafin; Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu na Kamfanin Dab’i na Northern Nigerian Publishing Company, Zariya – Najeriya.(1970) da kuma shafin internet mai suna Rumbun Ilimi