Wani doki na mutuwar karya idan bai son daukar mutum

Dokin a kwance lokacin da wani ke son hawansa
Dokin a kwance lokacin da wani ke son hawansa

Wani doki ya dauki hankalin jama’a a shafukan sada zumunta kan yadda yake kwanciya a kasa ya rufe idanu kamar ya mutu don kawai bai son daukar mutum.

Wannan doki ya samu magoya baya game da irin yadda yake yi. Dokin mai suna Jingang an kiyast cewa, “Ya fi kowane doki yin abu kamar almara.” Wadansu na kallon dokin kamar wanda aka horar don yin mutuwar karya idan bai son daukar mutum. Sai dai kuma wadansu na tunanin kawai dokin yana yin haka ne saboda wata baiwa da yake da ita, hakan ya sa wadansu ke sha’awarsa.

Duk lokacin da wani bako ya yi kokarin hawansa sai ya durkasar da gwiwoyinsa kasa, wani lokaci sai ya rufe idanunsa sai dai idan aka ga yana numfashi ne kawai za a fahimci ya yi hakan ne kamar yana wasa. Koda yana jin yunwa bai hana shi halinsa, kamar yadda wanda ya mallakin dokin ya sanar.

An dai fara wallafa bidiyon dokin ne tun shekarar 2015, wani mai suna Kenneth G ne ya wallafi bidiyon a kafar YouTube. Sai wani mutumin kasar Koriya ya yi martani, inda yake cewa dokin yana yin wannan halin nasa ne idan ya gaji da hawa daga mutane. Dokin yana sha’awar cin karas da shan sukari, amma idan ya gaji ya kwanta ko an ba shi ba zai tashi ba, kuma ko da zai mike sai ya fahimci ba kowa a wajen sannan ya mike. Wannan yana nuna matukar wayo da dokin ke da shi.

Kafar talabijin ta SBS na kasar Koriya ta Kudu da ta wallafa ta ce, an yi kiwon Jingang ne a gidan gona a kasar, kuma a cikin makonnin nan dokin ya ja hankali jama’a da dama bayan wani mai suna Fernando Salazar, ya sa bidiyonsa a shafinsa na Facebook inda sama da mutum miliyan 23 suka kalli bidiyon.

ADVERTISEMENT

Daya daga cikin masu maida martani ya rubuta cewa, “Wannan dokin yana yin haka ne idan bai bukatar wani ya matso kusa da shi, abin da dokin yake yi ba lalaci ba ne wayo ne kawai.” Wani kuma ya ce, “Dabarar dokin wata hanya ce ta kauce wa daukar nauyin wani abu.”

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya