✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani gajeren fim ya tada kura a Dubai

A makon jiya ne hukumomi a Dubai suka gurfanar da wani matashi dan shekara 22 a gaban kotu, bisa zargin laifin daukar hoton bidiyon yadda…

A makon jiya ne hukumomi a Dubai suka gurfanar da wani matashi dan shekara 22 a gaban kotu, bisa zargin laifin daukar hoton bidiyon yadda jami’an tsaro suka durfafi wani direban motar da ya aikata laifi.
Shi dai matashin, wanda aka sakaya sunansa, wanda kuma dan asalin kasar Indiya ne, ya yi amfani da kyamara ya dauki fim din yadda ta kaya tsakanin ’yan sanda da mai laifin, inda ya shiga intanet ya watsa shi ta ‘youtube’ kowa ya gani.
Kamar yadda Laftana-Janar Dahi Khalfan Tamim, Babban-Kwamandan ’yan sandan Dubai ya bayyana, ya ce abin da matashin ya aikata ya saba wa dokokin kasar, inda ba a amince wani ya dauki hoton bidiyon yadda jami’an tsaro ke gudanar da aikinsu ba kuma ya watsa shi ga al’umma.
A dokokin kasar Hadaddar Daular Larabawa, direban da aka kama da shi matashin da ya dauki bidiyon, idan kotu ta tabbatar da laifukansu, za su fuskanci dauri tare da tara.