✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani gwaji na riga-kafin coronavirus ya yi nasara

Wani kamfani a jihar Massachusetts ta Amurka mai suna Moderna ya samar da allurar riga-kafin cutar coronavirus wadda aka tabbatar da ita bayan gwaje-gwajen da…

Wani kamfani a jihar Massachusetts ta Amurka mai suna Moderna ya samar da allurar riga-kafin cutar coronavirus wadda aka tabbatar da ita bayan gwaje-gwajen da aka yi a kan wasu mutane.

Gwajin riga-kafin da aka yi mai suna mRNA-1273 ya nuna ya samar da garkuwa mai karfi a jikin mutum wanda hakan zai hana kamuwa da cutar.

Kamfanin ya bayyana cewa an kasa mutanen da aka yi gwaje-gwajen a kansu gida uku, inda aka ba su magungunan a matakai daban-daban.

A gwajin da aka yi, an baiwa wasu kwayoyin maganin 25, kashi na biyu aka ba su kwayoyi 100 inda sauran suka karbi kwayoyi 250.

Sakamakon ya nuna cewa wadanda aka bai wa kwayoyi 25 da 100 sun fi bada ingantaciyyar garkuwar da ta fi wadda aka samu a jikin wadanda suka warke daga cutar.

Wani labari da aka buga a shafin yanar gizo na WebMD ranar Litinin, ya rawaito kamfanin yana cewa yana shirye-shiryen gudanar da gwaje-gwaje na gaba wanda za a shigar da karin mutane nan gaba a bana.

Babban jami’i mai kula da harhada magunguna na kamfanin na Moderna, Tal Zaks, ya ce “Ina tunanin kimiyya tana nuna mana wannan ita ce kwakkwarar garkuwa kuma dole ne mu kiyaye ta”.

Ana gudanar da gwaje-gwajen ne da hadin gwiwar Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a kasar ta Amurka.

Akalla akwai yunkuri 90 da ake yi a wurare daban-daban da nufin samar da riga-kafin cutar inda shida daga cikinsu suka kai matakin fara gwaje-gwaje a kan mutane.