✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani hadarin mota ya halaka mutum 11 a Jigawa

Wani hadarin mota ya lakume rayukan wasu almajirai goma sha daya a Jihar Jigawa, tsakanin hanyar Gujungu zuwa Kano a ranar Litinin da ta. Hadarin,…

Wani hadarin mota ya lakume rayukan wasu almajirai goma sha daya a Jihar Jigawa, tsakanin hanyar Gujungu zuwa Kano a ranar Litinin da ta.

Hadarin, wanda ya yi sanadiyyar cinye rayukan mutane 11 da ake zatan dukansu almajirai ne kuma aka samu tabbacin cewar sun taso ne daga kauyen kawari da ke cikin yankin karamar Hukumar Kiyawa a Jihar Jigawa suna kan hanyarsu ta zuwa Minna a Jihar Neja domin neman ilimin karatun Alkur’ani.

Wakilimmu da ya halarci wajen da hadarin ya faru da misalin karfe 2.30 na rana kuma ya sami labarin cewar hadarin ya faru ne sakamakon fashewar daya daga cikin tayoyin motar ta bangaran direba ta baya saboda direban yana gudu sosai, wanda haka ya sa ya kasa sarrafa motar. Lamarin da ya sa motar ta fadi nan take, aka samu asarar rayuka masu yawa, wasu kuma da dama suka ji munanan raunuka masu yawa a jikinsu.

Kamar yadda bincike ya nuna, mutane tara ne suka sami raunuka, yayin da mutane bakwai suka suma. Haka kuma a lokacin da al’amarin ya faru, babu wani mutum da yake kusa da zai taimaka masu, domin kai su asibiti a ceci rayuwarsu.

Motarda ta yi hadarin, wacce kirar Toyota ce, tana dauke da yaran kanana, wadanda shekarunsu ba su wuce 12 ba, suna kan hanyarsu ce ta zuwa Jihar Neja.

daya daga cikin wadanda ke cikin ’yan uwan almajiran da suka mutu a sakamakon hadarin, Malam Yunusa ya ce za su tafi Jihar Neja ne domin neman karatu, shi ne wannan al’amari ya faru ga ’yan uwan nasa. 

“Mun ga tashin hankali marar iyaka, sakamakon faduwar motar. Ba mu taba ganin tashin hankali makamancin haka ba,” inji shi.

Kamar yadda wani mazaunin kauyan Balawa da ke kusa da kauyan Gamoji yake fada wa ’yan jarida a lokacin da al’amarin ya faru, ya ce tsawon shekaru masu yawa yana ganin hadarin mota amma bai taba ganin hadari mai muni kamar wannan ba.

Yayin da wakilimmu ya nemi jin ta bakin direban motar, wanda shi ya tsallake rijiya da baya, bai samu sukunin haka ba, kasancewar ba ya cikin natsuwar da zai yi magana da ’yan jarida. Haka kuma ya nemi jin ta bakin Kakakin rundunar ’yan sanda na Jihar Jigawa game da hadarin amma bai dauki waya ba.