✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Wani maganin kwarkwata na kashe kwayar coronavirus’

An gano cewa wani maganin kwarkwata yana iya kashe kwayoyin cutar coronavirus a cikin sa’o’i 48, amma a dakin bincike. Wasu masu bincike a Jami’ar…

An gano cewa wani maganin kwarkwata yana iya kashe kwayoyin cutar coronavirus a cikin sa’o’i 48, amma a dakin bincike.

Wasu masu bincike a Jami’ar Monash da ke Australia ne suka ce sun gano maganin mai suna Ivermectin yana iya kashe kwayar cutar da ke haddasa COVID-19.

Jaridar Daily Mail ta ruwaito daya daga cikin masu binciken, Dokta Kylie Wagstaff, tana cewa, “Mun gano cewa kusan maganin na kawar da kwayoyoyin halittar kwayar cutar a cikin sa’o’i 48; a cikin sa’o’i 24 ma yana matukar rage kwayoyin halittar cutar”.

Sai dai babu wata hukumar lafiya ta ba da damar yin amfani da maganin don yakar coronavirus.

Coronavirus ta yi ajalin likita a jihar Katsina

Coronavirus: ‘Yadda rayuwata ta kasance a killace’

Ko da yake ba a san yadda Ivermectin ke aiki a kan coronavirus ba, akwai yiwuwar maganin na hana kwayar cutar ne ta raunana karfin kwayoyin halittar jiki na kashe ta.

Mataki na gaba a binciken shi ne masana su gano adadin da ake bukata da zai dace da jikin dan-Adam na maganin don tabbatar da cewa idan aka yi amfani da shi ba zai cutar ba.

A cewar Dokta Wagstaff, “A duk lokacin da wata annoba ta addabi duniya, wadda kuma ba ta da magani, to idan akwai wani abu da aka riga aka hada zai taimaka wajen hanzarta gano bakin zaren.

“Amma a zahiri za a dauki lokaci kafin a samu riga-kafin da zai wadata”.

Masana kimiyya dai na sa ran za a dauki akalla wata guda kafin a fara gwajin maganin a kan bil-Adama.

Kafin a iya amfani da Ivermectin don yakar coronavirus dai, sai an yi gwaje-gwaje da dama a dakin bincike da kuma a kan majinyata.