Da Dumi Dumi

Wani matashi ya jefa motar BMW da aka ba shi kyauta cikin kogi

Wani matashi dan kasar Indiya mai suna Akash ya jefa mota kirar BMW da aka ba shi kyautar murnar zagayowar ranar haihuwarsa cikin kogi saboda ba ita yake bukata ba, inda ya ce shi kirar Jaguar yake so a saya masa.

An gano bidiyon motar tana ninkaya a cikin kogin a Arewacin Jihar Haryana ta kasar Indiya.

Daga baya ne motar ta makale a wani madakata da ke kogin, inda daga baya matashin ya yi kokarin ciro ta.

Yanzu haka ’yan sanda suna binciken lamarin, kamar yadda rahotanni daga Indiya suka nuna.

Mahaifin matashin, wanda yake bayar hayan gidaje ya ce, “Muna so ne mu ba danmu kyautar murnar zagayowar ranar haihuwarsa, amma kuma BMW ce za mu iya saya masa, amma shi ya dage dole sai Jaguar yake so, inda yake ta nanata cewa wai BMW din ta yi masa karama, amma mun zaci zai amshi motar idan mun saya. Shi ya sa mka sayo ta duk da ba ya so. Amma ba mu taba tunanin zai yi haka ba.”

ADVERTISEMENT

An samo wannan rahoton ne daga bbc.co.uk

Share