✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani mutum da yayi tatul da giya ya hallaka kwamandan soji

Kwamandan Bataliya ta biyu ta rundunar sojin Najeriya da ke Kaduna Lt. Col. Abraham Gbileve ya gamu da ajalinsa a lokacin da ya halarci wata…

Kwamandan Bataliya ta biyu ta rundunar sojin Najeriya da ke Kaduna Lt. Col. Abraham Gbileve ya gamu da ajalinsa a lokacin da ya halarci wata mashaya shi da abokinsa domin shakatawa.

Majiyarmu ta ce bayan sun kammala shan giya a mashayar sun shirya za su koma gida, sai abokin kwamandan ya shiga mota yayo baya da ita domin ya dauki abokinsa kwamandan sojin.

Ko da yayi baya da motar bai kula ba sai ya take abokin na shi dake zaune bisa kujera lamarin da ya faru a ranar Talata 26, ga watan Mayu.

Majiyar tace rundunar soji na tsare da abokin kwamanda an kuma gudanar da bincike akan faruwar lamarin wanda ya abku a garin Makurdi a jihar Benue, mahaifar kwamandan sojin.

Marigayin yaje jihar Benue hutu ne, inda ya aiki direbansa tare da dogarinsa, jinkirin da direban yayi bai dawo ba, sai abokinsa yayi niyar ya rage masa hanya, lamarin da yayi sanadiyyar kade shi a motar.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na gwamnatin jihar Kaduna, a shafinsa na sada zumunta ya bayyana Marigayin a matsayin zakakurin hafsan soji mai kwazo da iya aiki da kuma hulda da jama’a, mai kishin kasa da sanin ya kamata.

Yace Marigayin ya taka rawa wajen magance matsalar ‘yan bindiga a jihar Kaduna.