✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani ya rasa gidansa a caca a wasan Manchester United da Arsenal

Wani dan Uganda mai suna Henry Dhabasani wanda yake goyon bayan kulob din Arsenal da ke Ingila ya rasa gidansa a wata caca da ya…

Motar da Rashid Yiga ya sa a cacar da suka yi da Henry Dhabasani Wani dan Uganda mai suna Henry Dhabasani wanda yake goyon bayan kulob din Arsenal da ke Ingila ya rasa gidansa a wata caca da ya yi  da abokinsa mai suna Rashid Yiga mai goyon bayan kulob din Manchester United da ke Ingila.
Mutanen biyu sun yi cacar ce kafin a buga wasan Arsenal da United a gasar rukunin Premier kimanin makwanni biyu da suka wuce.
An ce Henry Dhabasani ya sha alwashin sanya gidansa mai dakunan kwana biyu watau (two bedrooms flat) yayin da shi kuma Rashid Yiga ya sanya motarsa da matarsa.
Rahotannin da jaridar The Obserber da ake wallafata a Uganda ta ce mutanen biyu sun kulla yarjejeniyar ce a rubuce kuma a gaban jama’a don su zama shaida.
Bayan an tashi wasan, kulob din Manchester United ne ya samu nasara a kan na Arsenal da ci daya babu ko daya, al’amarin da ya sa Rashid ya mallaki gidan Henry mai dakunan kwana biyu.
Rashid ya gode wa dan kwallon Manchester United mai suna Robin ban Persie a kan kwallo daya tilo da ya zura a ragar Arsenal a wasan da hakan ta ba shi damar lashe cacar da suka yi da abokinsa Henry.
Rahotannin sun tabbatar jim kadan da tashi wasan, magoya bayan United suka yi wa gidan Henry tsinke inda suka tilasta shi kwashe kayansa da iyalinsa don abokinsu Rashid ya mallake gidan kamar yadda suka kulla yarjejeniya tun farko.
Tuni Henry Dhabasani ya shiga cikin halin kaka-ni-ka yi bayan ya rasa gidansa kuma yanzu haka ya fara rokon al’umma su taimaka masa da kudin sayen wani.