✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani yaro ya kubuta daga hannun matsafa

Wani yaro dan shekara daya da wata uku da haihuwa mai suna Musa Shamsu da ke garin Unguwar Jumare a kusa da garin Saminaka da…

Wani yaro dan shekara daya da wata uku da haihuwa mai suna Musa Shamsu da ke garin Unguwar Jumare a kusa da garin Saminaka da ke Karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna ya kubuta daga hanun wasu matsafa, bayan da suka sace shi suka tafi da shi zuwa wani kangon gida, suka farke cikinsa. Amma suka tafi suka bar shi haka, kuma aka zo aka same shi da ransa.

Da yake yi wa jaridar Aminiya karin bayani kan wannan al’amari, kakan yaro, mai suna Malam Musa Shitu Unguwar Jumare ya ce bayan ya fita daga gida da safe a ranar Litinin din da ta gabata, zuwa karfe 11 na rana ya dawo gida sai aka ce masa ba a ga wannan yaro ba, bayan da ya fito kofar gida yana rarrafe.

Ya ce sun yi ta neman wannan yaro a wannan gari da bayan gari har ya zuwa gefen rafi na wannan gari, amma ba su gan shi ba, har zuwa daren wannan rana.

‘’Bayan da gari ya waye wajen karfe tara da rabi na safe, sai wani sirikina ya ce mu je mu cigaba da dubawa. Muna cikin dubawa sai Allah Ya taimakemu muka ga wannan yaro a cikin kangon wani gida, a bayan garin a tube shi an farke cikinsa ga hanjinsa a waje, amma bai mutu ba’’.

Malam Musa ya yi bayanin cewa daga nan, sai suka dauko shi suka kai shi asibiti aka ci gaba da jinyarsa.  Ya ce lokacin da suka je asibitin  suka ce za a biya Naira dubu 50 kuma sai an ajiye Naira dubu 20 kafin su taba shi. Suka je suka nemo ba shi suka kawo masu.

Ya ce yanzu dai yaro yana samun sauki, sai bashin kudin da ake binsu na jinyar da aka yi masa.

Ya yi addu’a Allah Ya tona asirin wadanda suka yi wannan abu.

Daga nan ya roki Karamar Hukumar Lere da sauran jama’a su tallafa masu, domin su biya bashin kudin maganin da ake yi wa wannan yaro.

Wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan  Jihar Kaduna, ASP Yakubu Sabo domin jin ta bakinsa kan wannan al’amari, inda ya yi wa wakilinmu alkawarin zai bincika ya kira shi ya yi masa bayani, amma har ya zuwa rubuta wannan labari bai kira ba. Kuma wakilin namu ya sake kiransa amma bai same shi ba.

Amma wata majiya a ofishin ’yan sanda na garin Saminaka ta tabbatar da cewa tuni an tura wannan al’amari zuwa sashin binciken aikata laifaffuka na rundunar ’yan sandan  Jihar Kaduna, domin ci gaba da bincike.