Categories: Kwalliya

Wankan rage gajiya domin damina

Tunda damina ta kan-kama, ya kamata mu san irin ruwan da za mu yi amfani da shi. Sau da yawa za ku ga wasu kuraje na feso wa mutum musamman a lokacin damina. Irin hakan na faruwa ne sakamakon yin wanka da ruwan sama.

Fatar mace ya kamata ta zama mai laushi da santsi saboda hakan na kawo wasu sinadarai da za ku sa a cikin ruwan wanka domin rage gajiya da kuma samun fata mai laushi a lokacin damina.

ADVERTISEMENT

Sinadirai

 • Sabulu marar kamshi ko sabulun jarirai (baby soap).
 • Man Rosemary, za ku iya samun wannan a shagunan da ake sayar da nau’o’in man kwalliya.
 • Ruwa .
 • Man Rose Water za ku iya samunsa a inda ake sayar da kayan kwalliya.
 • Man Glycerin.

Amfanin sinadiran

ADVERTISEMENT
 • Man Rosemary na rage rikewar jijiyoyi kuma na kara karfin jiki.
 • Man Glycerin na sanya santsin fata musamman ga mai gautsin fata.
 • Sabulu na cire dattin jiki.
 • Turaren banilla na sanya wa ruwan kamshi.

Hadi

 • A dauki sabulu daya sai a sa shi a kwalba, sannan a sanya man glycerin a cikin kwalbar. A rika girgiza kwalbar sai a bar hadin na tsawon minti biyu zuwa uku.
 • Sai a zuba ruwa a cikin hadin.
 • A diga man Rosemary a cikin hadin.
 • A zuba turaren banilla a cikin hadin domin samun kamshi mai kyayatarwa.

Bayan an gama wanka, sai a zuba ruwan dumi a jiki domin wanke kumfan da ke kan fata.

. .

Recent Posts

Kirkiro Masarautun Kano: Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunci

Babbar kotun jihar Kano ta tsayar da ranar 14 ga Nuwamba 2019, a matsayin ranar da za a yanke hukunci…

1 hour ago

An yi arangama tsakanin ‘yan Kwankwasiyya da Gandujiyya a Kano

Akalla mutum takwas ne suka samu raunuka yayin da aka lalata motoci 10 a yau Litinin lokacin da aka yi…

2 hours ago

Kotu ta daure direba kan zargin yi wa agolarsa ciki a Abuja

Wata Kotun lardi ta birnin tarayya da ke Garin Jiwa Abuja, ta bada umarnin tsare wani direba mai shekara 36…

5 hours ago

’Yan bindiga sun tarwatsa kauyuka 16 sun kashe ’yan banga 3 a Kaduna

Al'ummar Karamar hukumar Igabi da ke a jihar Kaduna sun waye gari cikin tashin hankali inda wasu ’yan bindiga suka…

5 hours ago

An rantsar da sabon Mataimakin Gwamnan Kogi

Duk an kammala shirye-shiryen rantsar da Edward Onoja a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan jihar Kogi. Babban alkalin jihar Nasir Ajanah,…

11 hours ago

Yau Buhari zai ziyarci kasar Rasha don halartar taro

A yau Litinin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, zai ziyarci birnin Sochi a kasar Rasha don halartar taron  kwana uku wanda…

12 hours ago