✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ware Naira biliyan 37 don gyara ginin majalisa

Idan aka yi la’akari da halin kuncin da ’yan Najeriya suke ciki a yanzu da rashin abubuwan more rayuwa kamar ingantattun asibitoci da makarantu da…

Idan aka yi la’akari da halin kuncin da ’yan Najeriya suke ciki a yanzu da rashin abubuwan more rayuwa kamar ingantattun asibitoci da makarantu da hanyoyi da tsabtataccen ruwan sha da sauransu musamman a Arewa wacce ita ce koma-baya wajen ci gaba  kuma daga wannan yankin ne Shugaban Kasa Buhari ya fito, abin Allah wadai ne a ce gwamnatinsa ta amince da ware  makudan kudi har Naira biliyan 37 don gyaran majalisa. Sanin kowa ne a tarihin kasar nan ba gwamnatin da talakawa ke ba ta uzuri sosai irin wannan gwamnati, saboda soyayyar da suke nuna wa Shugaba BuharI, Amma al’amura sai sauyawa suke a kwan a tashi. Da a ce talakwa sun samu kwatankwacin soyayyar da suke wa wannan gwamnati to da ya yanzu rayuwarsu ta canja.

Yana da kyau Shugaba Buhari ya tuna irin wahalar da talakawa suka sha don ganin ya samu shugabancin kasar nan, ta wajen maida hankali a kan ayyukan da za su amfani talakawan kai-tsaye. Bai kamata duk wahalar da ’yan Najeriya suka sha a baya wajen kafa gwamnati su tashi a tutar babu ba. A ce kullum su ne da turin mota kuma bayan ta tashi ta bule su da kura. Abin mamaki shi ne ana ware kudade don wasu ayyukan amma da wuya ka ga ayyukan sun samu a lokacin da ya kamata. Wasu lokutan ma ayyukan ba sa samuwa da yake talaka ne zai mora kai-tsaye. Amma wannan kudi da aka ware don gyaran majalisa da yake su zai amfana nan da nan za su zartar da su don biyan bukatarsu.

Idan ka dauki bangaren kiwon lafiya an ware Naira biliyan 46 ne duk fadin Najeriya, bangaren ilimi kuma Naira biliyan 48, amma gyaran Majalisar Dokoki ta Kasa  da ke Abuja a waje daya zai lakume har Naira biliyan 36.

Idan ka dauki bangaren kiwon lafiya misali, kamar yadda wannan jarida ta Aminiya ta yi wani nazari Naira biliyan 37 za ta gina kananan asibitoci na PHC guda 27,000 a fadin Najeriya, to idan aka auna alfanun gina asibitocin da gyaran majalisa a mahangar hankali kuma aka sa a faifai ba sai an fada wa mutum wanne ya fi muhimmanci ba, duk da cewa shi ma bangaren lafiyar an ware masa nasa kudin. Abin dubawa a nan shi ne shin kudin da aka ware don kiwon lafiya da kuma muhimmancin da inganta harkar lafiyar ke da shi ya isa a magance matsalolin kiwon lafiya a kasar nan ko kuma rage matsalolin da babban kaso na matsalolin?

Amsa ita ce a’a, bangaren kiwon lafiya a kasar nan ya tabarbare sosai har ta kai ga asibitici da dama ba magunguna, ba gadaje, ba kayan aikin kuma ba  likitoci. Kai hatta gine-ginen wasu asibitocin ma sun tsufa suna bukatar gyara ko sabuntawa.

Wannan kau da kai da halin ko in kula a kan muhimman abubuwa kamar kiwon lafiya da ’yan kasa ke bukata da shugabanni ke yi na faruwa ne saboda su ba a duba lafiyarsu da ta iyalansu a Najeriya. Don hakan ma da yawansu ba su san halin da talaka ke ciki ba, ko kuma sun sani kawai suna shakulatin-bangaro ne da abin. Ko kuma suna gina nasu asibitocin kudin don haka suke gudun a inganta na gwamnati. To ko ma dai mene ne yana da kyau su tuna cewa an zabe su ne don su yi wa kasa aiki ba tara dukiya ba.

Idan aka dawo bangaren ilimi ma haka abin yake, akwai makarantun gwamnati da ba su da isassun kujerun zama, wasu ba su ma da aji a karkashin bishiya suke darasi. Matsaloli dai ga su nan bila adadin kuma wadannan makarantu suna wuraren da ke karkashin wakilcin wani sanata ko dan majalisa ne, amma bai damu ba. Kuma ba za ka ji shi wajen nema wa mutanen da yake wakilta wani abu ba, amma da zarar an kawo dokar da ta shafe su za ka ga suna kan gaba wajen dabbaka ta.

Akwai bukatar a gina sababbin makarantu a wurare da dama a kuma gyara wadanda suke bukatar gyara, a samar da kayan aiki ga malamai, a ba su kulawa ta musamman don su samar da ilimi mai inganci.

Wannan kadan ke nan idan ka dauki iya bangarorin biyu ka yi fashin baki ko sharhi a kan abin da ya fi dacewa a yi a kasafin kudi da kuma wane bangare ya fi dacewa a bai wa kaso mafi tsoka na daga kasafin kudin, wannan majalisa a yadda take a yanzu ba ta da wata bukatar gyara tunda ba wani abu nata da za a ce ya lalace da har zai hana a yi zama a cikinta. Sabanin wasu asibitoci da ake kwantar da marasa lafiya a kan tabarmi, ko ajin da ba wani gini da za a ce wannan aji kaza ne sai karkashin bishiya.

Akwai wasu bangarorin ma da haka abin yake suna da bukatar gyara kuma kamata ya yi a karkatar da wannan kudin gyaran majalisar don gina kasa. Gyaran majalisa dai bai da wani muhimmanci in aka kwatanta da sauran abubuwan da suke da bukatar gyara a kasar nan.

Wannan zai sa a gane cewa shi talaka ba ta shi ake ba a kasar nan, shi bai da wata gata, kuma bai da wani amfani a wajen shugabanni da ya wuce kada kuri’a lokacin zabe, daga nan kuma shi ke nan.

Don haka ina kira da babbar murya ga shugabanni su yi kokari wajen yin adalci, su kuma talakawa  su farga su san irin shugabannin da za su zaba kada su bari ana yaudararsu lokacin yakin nema zabe da kudi ko kayan masarufi da ba su taka-kara sun karya ba. Don duk wanda ya yi musu haka tamkar ya sayi ’yancinsu ne kuma a matsayinka na talaka in ka sayar da ’yancinka to shakka babu ba wata ribar dimokuradiyya da za ka mora ko an kafa gwamnati.

Anas Muhammad Sulaiman Dukku, Dukku LGA, Jihar Gombe (07068743859)