✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasan Wazamai dabaru ne ba tsafi ba – Sarkin Wanzamai

A ranar Asabar da ta gabata ce Kungiyar Wanzamai ta Abuja ta gudanar da bikin Wasan Wanzamai wanda ya hada da nuna bajinta da aska…

A ranar Asabar da ta gabata ce Kungiyar Wanzamai ta Abuja ta gudanar da bikin Wasan Wanzamai wanda ya hada da nuna bajinta da aska da sauransu. Amniya ta zanta da Sarkin Askar Abuja, kuma Shugaban Kungiyar Wanzamai ta Najeriya Alhaji Ahmad Rabo Magaji inda ya yi bayanin a kan sana’ar da kuma wasan nasu:

Mene ne takaitaccen tarihinka?

Sunana Ahmad Rabo Bawa Magaji, Sarkin Askar Abuja kuma Shugaban Kungiyar Wanzamai ta Najeriya. An haife ni a garin Garki na nan Abuja a unguwar da a ka fi sani da Unguwar Kurmi a lokacin. Sai dai an ta da ita a yanzu tun a lokacin da a ka zo aikin gina rukunin gidajen ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa (Apo Lagislatibe Kuarters). Mahaifina ya taso ne daga kauyen ’Yandakan-Ruma da ke Karamar Hukumar Batsari a Jihar Katsina, ya kuma taho nan Abuja ne tare da mahaifinsa da kakansa domin wannan sana’a ta wanzanci. Ka ga ke nan gadon sana’ar na yi.

Wace nasara ka samu a wannan sana’a?

Babbar nasarar da zan ce na samu ita ce na aikin jinkai da nake yi ga al’umma ta hanyar yi wa mutane magunguna irin namu na gargajiya. Wani abu da ba zan manta ba shi ne, wani da ciwon daji ya ci karfinsa ya rika yin habo ba tsayawa, an kawo shi wajena daga garin Mararraba bayan ya shafe kwana 3 a asibiti ba tare da an samu nasara ba. Amma ba mu wuce minti 5 zuwa 10 ba, sai Allah Ya dauke jinin. Haka ana kawo min jariri in cire masa beli ko in yi masa kaciya ko gurya. Akwai malaman asibiti da dama da ke turo min jama’a saboda gamsuwa da aikina, sun ce idan na yi kaciya bai wuce minti 2 zuwa 3 jini ya dauke kuma yaro ba ya kuka. Idan ma karaya ce duk harkar wanzanci ce, idan na yi dori a hannu ko a kwarkwaron kafa mako 1 zuwa 2 shi ke nan Allah Ya karba idan ya yi nauyi ne mako 3 a warke.

Wace matsala ka taba fuskanta a sana’ar?

Alhamdu liillahi, kalubalen da ba zan manta ba shi ne wani taimako da na yi ga wani amma sai abin ya koma fitina har ya kai ga ana neman za a tsare ni a ofishin ’yan sanda. Yadda abin ya faru shi ne, matar wani dan sanda ce ta zo da wani jariri wajena yana fama da ciwo na kaduwa yana ta suma. Sai na yi masa jinya ya samu sauki, amma a karshe maimakon a biya ni hakkina sai abin ya koma fitina har ana shirin za a tsare ni. Sai maigidan dan sandan wani da ake kira Libata wanda a yanzu ba ya raye, ya samu labari ya iso ofishin. Yana zuwa sai ya kai masa mari sannan ya rika yi masa fada ya kuma tilasta masa ya biya ni hakkina. To hakan ya yi matukar tayar min da hankali saboda ban taba fuskantar rikicin da ya shafi na ’yan sanda ba sai a ranar. Sai kuma wata rana wadansu yarana suka yi wa wani dan soja aiki aka samu akasi jini ya rika zuba. An garzaya da yaron asibiti sannan aka je aka kama yarana aka tsare su. Bayan na samu labari sai na kai kaina na ce a sake su, ni sai a kama ni, saboda ni ne maigidansu. Amma sai shugaban ’yan sandan ya ce ba maganar kamu ba ce, ka je ka yi jinya ga yaron idan ya warke shi ke nan. Na je na yi amfani da wani garin magani na wanke wurin na matse na fid da jini na ba shi wani ya kurkura cikin minti 2 zuwa 3 Allah Ya taimaka jini ya tsaya.

Wanzamai na ba da gudunmawa ga rayuwar al’umma, ko kuna samun wani tallafin hukumar?

Wannan na daga cikin dalilan da suka sa na shiga harkar ’yan siyasa don jawo gwamnati ga al’ummar da nake shugabata kuma wannan taro da ka ga mun shirya yana ciki. Kuma mun gayyato jami’an gwamnati da ’yan siyasa zuwa wannan gangami namu don su san irin gudunmawar da muke bayarwa ga al’umma. Kuma wannan sana’a ba ta hana ni yin noma da kiwo ba, wanda a dalilin hakan ina taimaka wa kungiya da shi ta hanyar daukar nauyin wadansu.

A yayin jawabinka ka bayyana dalilin da ya sa ba za ku daina tsafi ba. Da ma kuna sa tsafi a sana’ar ce?

Wannan na fade ne a matsayin gishirin magana don kalami ya yi dadi. Ai matsafi yana nan gindin tsafinsa, mu kuma muna yin ’yan dabaru ne. Dabarun nan kuwa shi ne mu hada kamar ja da fari sai ya koma baki. Mu kuma hada fari da baki ya koma ja. Sa’annan idan muka hada wasu dabarun za mu sa kamar namiji ya yi nakuda ya haihu. Za mu iya cire kan akuya mu sa mata na kare ta kuma yi tafiya, za mu kira jini ya zo nan ya gaida mu iya gwargwado, mu ce ya koma. Za mu sa yaranmu su harba allurai su zo sannan mu sa wani yaron ya bude hannunsa ya karba ya maida su. Duk wadannan dabaru ne na yau da kullum da muka gada daga wajen iyaye da kakanni. Idan ka bi za a bi ka, idan kuwa ba ka bi ba, to ba za ka zama mai asirin babanka da kakanka ba.

To wane dalili ya sa ba za ku bar wadannan ayyuka ba koda kuwa sun yi karo da Musulunci?

Ba mu ce ba za mu bari ba. Ya yi karo da shari’an musulunci amma kuma ai Allah Ya ce tashi in taimake ka. Idan zan fada maka wani labari ka yarda, an fuskanci matsalar Boko Haram mai muni a baya. A lokacin da matsalar ta yi kamari wanzami aka sa ya yi jagora, suna harbinsa yana kakkabe harsashi har ya samu nasara ya kama shugaban. Idan da ya je haka nan ba tare da daukaR wani mataki ba, da ba a samu nasaraR nan ba. Ka ga kuma ai wannan abu da ya yi ya samu nasara har Musulmi sun samu dama sun yi Sallah. To ashe kuwa idan ma kuskure ne ai kuma an samu gyara, kuma ma ai ba wani abu ne muka ajiye mu ka ce Allah ne ba. Mu dai muna ’yan dabaru ne kuma mun san Allah dai Shi ne Allah. Sannan idan za mu yin kuma muna cewa mun bai wa Allah zabi idan Ya yarda bukatunmu su biya idan kuwa Allah bai yarda ba fa ni’ima. Sai dai duk yadda dan Adam zai wanke mutum, mutum ba zai wanku ba saboda shi Allah Yana amfani ne da zuciya.