Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Wasika ga Gwamnan Kano kan Masarautar Kano

Bayan gaisuwa da girmamawa na rubuto  maka wannan wasika ce,  don in shaida maka tunanin al’ummar da ke wajen Kano kan abin da ke  faruwa a Kano  a tsakanin gwamnatinka da Masarautar  Kano.

Da  farko  ina son ka sani  Kano  cibiya ce ta  duk  Hausa/Fulani  da ke  duniya.  Cikin Hausa/Fulani goma na  duniya biyar na da alaka da Kano ko ta auratayya, jini, asali ko kasuwanci ko wata  hulda mai karfi.

ADVERTISEMENT

Duk jihohin da ke da makwabtaka  da Kano suna da alaka ta kut-da-kut da Kano  ta daya daga abin da na fada a baya. misali a jihata Katsina. Yankin Sanatan  Funtuwa mafi  yawansu asalinsu  Kanawa ne. Haka  yake  a yankin Sanata  ta Daura, hatta Katsina a da tana karkashin Kano ne a zamanin mulkin Turawa.

A  Katsina ta Tsakiya, kusan  gida takwas cikin goma na da wata alaka da  Kano, ta  auratayya, jini, asali, ko kasuwanci ko wata  hulda mai karfi. Ni marubucin nan  tsatso ne daga jinin zuriyar  Malam Muhammadu Bakatsine, da ’yar uwarsa Malama Jibado wadanda Katsinawa ne a asali amma da su aka yi  jihadin  Shehu Usman Dan Fodiyo a Kano kuma  sun taka rawa  sosai kamar  yadda  tarihi ya tabbatar.

ADVERTISEMENT

Wadannan dalilai  suka  sanya, duk  abin da ya  shafi Kano duk  duniyar  Hausa/Fulani kan amsa kuma yakan zama kamar amo ko’ina ka ji ya dauka a kan shiga damuwa kan lamarin sosai.

Yallabai, kana ba ni  tausayi, don ana misalta ka da mutumin kirki, mai hakuri wanda  miyagun mutane ke sarrafawa, don  haka wani  lokaci  sai ka dauki matsayi bisa kuskure a lokacin da bai  dace ba sai ka zama ba ka da goyon baya.

Rabuwarka da Kwankwaso, an  dauka kai ne ka yi butulci don Kwankwaso  ya kasance  tare da kai a duk tsawon zamanku  shekara takwas yana rike da mukamai  ba ku da gwamnati a Kano. Ka yi ta daukar matsaya ta tafiyar da mulkin Kano wadda ta yi ta jawo maka karin bakin jini ga duk wani  mataki da ka dauka, misali gina shaguna a filin Idi, da ginin  gadar  kasa a hanyar  Zariya.

Hoton bidiyon da ake  zargin kai ne, inda wani mutum na ba ka Dalolin Amurka a matsayin cin hanci da hana binciken don tabbatar da gaskiyar hotunan ya sa alamar  tambaya  da yawa a kanka. Fara daukar  mataki a kan Masarautar Kano a cikin watan Ramadan  ya  daga wa duk  Musulmi hankali  ya kuma zama abin magana a wata Mai alfarma. Wannan ma  ya jawo maka bakin jini ba dan kadan ba.

Duk wanda ke bin yadda lamura ke  gudana a tsakanin gwamnatinka da  masarautar, ya san ba ikhlasi a ciki  sai dai wani aiki  don huce takaici wanda wadansu ke zugawa ana yi.

Duk  kuma abin da ba Allah  ba ne asalinsa  ba ya  dorewa  ko  ba jima ko ba dade. Babban abin da ya kamata mutum ya  fara kawowa a gabansa ga duk abin da  zai  fara  shi ne tarihin da zai  bari, wanda  kuma zai  rika bin sa da farautarsa ko bayan ransa.

Wace nasara aka samu da  matsayar gwamnatin Kano  ga masarauta? Rarraba kan al’umma daya mai karfin gaske,wadda ke magana da murya daya a da.

Kashe dimbin kudade don gaisuwa da wayar da kan mutane a kan matsayar da gwamnati ta  dauka a kan masarautar, wanda  duk mai bin shirye-shiryen rediyo da sauran kafofin  sadarwa ya san ana kashe kudaden da suka kamata a saka su wani wajen da ya dace.

Kashe kudade don kawai a inganta sababbin masarautu, wadanda ya kamata a saka su  a wasu  ayyukan gina al’umma da ya fi dacewa. Dauke hankalin al’ummar Kano daga gaskiyar  abin da ke ci musu tuwo a kwarya  zuwa tattauna abin da ba zai amfani rayuwarsu kai-tsaye. Duk a wannan ba inda talaka  zai amfana,  sai dai  Ranar  Hawan Sallah  Karama da Babba a yi a inda ya fito sai kuma Ranar  Juma’a a je Sallah da kuma  zaman fada.

Saboda  kowa  ya san cewa, a  mulkin  dimokuradiyya Kansila, Ciyaman, Dan Majalisar Jiha, na Tarayya da Sanata su ne  kai- tsaye  suke magana a kan al’ummarsu ba wani Sarki ko wata  sabuwar masarauta ba.

Yallabai, wata rana za ka  bar  mulkin kuma bayan nan Allah ne Masanin wa zai amshe ka, kuma ya maye tsarinsa. A lokacin duk masu zuga ka za su  guje maka. Wannan abin da ake  wata rana kai za ta  dawo maka da iyalinka kai ne za ai ta kawo  tarihi ana danganta shi da kai, a lokacin kowa zai juya maka baya yana  fadin cewa  kai ne ka  sanya  shi.

Yana da  kyau  a  saka hangen nesa a kuma sanya kula  komai mutum zai gabatar ya tuna cewa wata rana yaya abin zai  dawo masa kuma ya zama masa  tuhuma, mai ba da shaida  kuma alkalin kansa da kansa.

A kan bincike na  masarauta, a  wannan zamanin da muke ciki wane ne za a bincika ya tsallake  ba a same shi da laifi ba?  Wata  rana za ka bar mulkin kana fata a yi maka binciken kwakwaf?

Bincike don bata suna bai hana abin da Allah Ya tsara  bawa zai yi nasara a kansu na  rayuwa, misali zamanin Abacha  na  Shugaban Kasa, ya sanya  an yi wa tsohon Gwamnan Kano Kabiru Gaya binciken terere wanda  aka rika yada  abin a gidan rediyo kai-tsaye da  ba da  labarin  a sauran kafofin watsa labarai yanzu  Kabiru  Gaya  Sanata ne,  daga Jihar Kano a karo  na uku. Ina rokon a sa hankali, lura da hangen nesa don gaba don wata rana ko don zuriya da iyali da  sauran al’umma.

Danjuma Katsina

Mawallafi ne kuma dan jarida

Ana iya samunsa a: mdanjumakatsina@gmail.com 08035904408