Da Dumi Dumi

Wasika: Yadda Obasanjo ya nemi firgita Buhari

Wasika: Yadda Obasanjo ya nemi firgita Buhari
Wasika: Yadda Obasanjo ya nemi firgita Buhari

Tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo ya yi kokarin firgita Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a wasikar da ya aike masa a farkon wannan mako, inda ya gargade shi cewa Najeriya ta kama hanyar fadawa a cikin bala’i gadan-gadan kuma Buharin ne kawai zai iya hana ta hakan idan ya so.

Cif Obasanjo, ya sake rubuta wa Shugaba Buhari wasika ce, ta biyu a bana, inda ya nuna Najeriya za ta iya zama Rwanda ta biyu inda fadan kabilanci zai iya gwara kan mutanen kasar saboda abin da ya kira kisan da kabilar Fualni suke yi ga sauran jama’ar kasar nan.

Ana iya cewa dai kisan Funke Olakunrin mai shekaru 58 ne ya tunzura Obasanjo ya rubuta wasikar.

Funke dai ’yar Reuben Fasoranti ne, wani mai fada -a-ji a kabilar Yarabawa.

Shugaba Buhari da Rundunar ’Yan sandan Najeriya sun yi Allah wadai da kisan Misis Olakunrin, kuma Shugaban Kasar ya sanar da yin garambawul a bangaren tsaro kan manyan tituna a Kudancin kasar nan.

ADVERTISEMENT

Cif Obasanjo ya ce kashe-kashe da rikice-rikice na ci gaba da zame wa Najeriya bala’i, ga kuma babbar matsalar wutar kabilanci da ke ruruta bayan hawan Buhari mulki shekara hudu da suka gabata.

Obasanjo ya ce an shafe shekaru masu yawa rabon da Najeriya ta samu kanta a cikin irin wannan masifa da ake fama da ita.

A cikin wasikar Obasanjo, ya shaida wa duniya cewa Najeriya ta kamo hanyar aukawa cikin kashe-kashen da idan ba a yi da gaske ba, to zai yi wuya a iya kashe gobarar.

Obasanjo ya jero wasu abubuwa 11 a cikin wasikar kamar yadda BBC ya ruwaito da suka hada da:

1 – Rugujewar Hadin kan kasa

Zan yi magana ne dangane da halin ko-a-mutu-ko-a-yi-rai da muke ciki, wanda ya shafi kasarmu baki daya. Wannan matsala an bar ta tana ta kara ruruwa, har ta ci karfin ginshikan da suke rike da wannan kasa tun lokacin da aka kafa ta. Tuni tubulan da suka gina hadin kan kasar nan an fara ruguza su.

Na shiga damuwa da tsoro sosai ganin cewa a yanzu tura ta kusa kaiwa bango, mun kusa kaiwa inda ba za mu iya jan linzami mu tsaida bala’in da ka iya tunkarar kasar nan ba.

Dole ne in nuna damuwata, domin a matsayina na dan Najeriya, a yanzu haka da tabon raunin Yakin Basasa zan mutu a jikina. Haka shi ma da na da tabon raunin yakin Boko Haram zai mutu a jikinsa.

2 – Yanke kaunar samun tsaro daga gwamnati

Idan jama’a ta yanke kauna daga tunanin samun tsaro daga gwamnati, to sai su bi duk wata hanyar da su ke ganin ita ce mafita don nema wa kansu tsaro. Ko dai mutum ya nemi tsare kansa ko ta halin kaka, ko kuma gungun jama’a su nemi hanyar tsare kansu ta kowace hanya. Kowa sai ya nemi tasa da za ta iya fisshe shi ke nan.

3 – Karyar kakkabe Boko Haram

Sama da shekara goma ke nan ana fama da Boko Haram. A cikin shekarun nan goma kuwa, hudu a cikin gwamnatinka aka shafe su. A kullum Boko Haram sai ta’asa suke yi, duk kuwa da karyar da gwamnatinka ke ta kantarawa cewa an gama da Boko Haram. Kalaman da Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya ya yi kwanan nan, inda ya yi korafin cewa sojoji ba su da kuzari ko kishin yaki da Boko Haram, wata magana ce da ta amsa kanta da kanta dangane da halin da ake ciki a kan Boko Haram.

Duk abin da ka ga dama ka je ka ci gaba da fada wa mutane, amma kowa ya san cewa Boko Haram na nan daram, kuma a kullum suna kashe mutane, suna sace mutane da yin garkuwa da su, su yi fyade, kuma su kama mutane a matsayin bayi suna sayarwa. Wadansu kuma suna tilasta su shiga harkar Boko Haram, ta hanyar dana musu bam domin su shiga cikin jama’a su tarwatsa su.

Sannan ina tabbatar maka da sanda da duka kadai ba za a iya korar Boko Haram ba. Saboda ta yaya za ka iya kakkabe Boko Haram a Arewa alhali kashi 50 cikin 100 na yankin Arewa maso Gabas ba su da ilimi? Ta yaya za ka kakkabe Boko Haram alhali kashi 70 cikin 100 na yankin ba su da aikin yi?

4 – Ta’azzarar rikicin makiyaya da manoma

Rikicin makiyaya da manoma da aka ki ba muhimmancin magance shi, yanzu ya yi muni kwarai. Ya tashi daga rikici ya koma hare-hare, samame, garkuwa da mutane da sace su, fashi da makami, kashe-kashe a duk fadin kasar nan.

Babban abin takaicin shi ne yadda wannan barna da ake tafkawa ake yi mata kallon cewa Fulani ne ke yin ta tare da daurin gindin Fulani manyan kasar nan a yankuna daban-daban.

Karin abin bakin ciki shi ne yadda ’yan Najeriya da dama da wadanda ba ’yan Najeriya ba ke kallon cewa kai ne aka dora wa dukkan laifin abin da ake aikatawa, a matsayinka na Bafulatani. Wani lokaci dai hasashe kan zama gaskiya.

5 – Fulani su fito su fadi korafinsu a zauna a duba

Akwai bukatar Fulani su fito su fadi dukkan korafe-korafen da suke da su. Idan suna da hujja, sai a zauna a shawo kan matsalar. Idan akwai wasu kabilu masu wani korafi, su ma su fito su bayyana nasu. Sai a zauna a baje komai a kan tebur a nemi maslaha.

6 – Lokaci na neman kurewa

Bai kamata a rika yi wa komai rikon-sakainar-kashi ba, saboda lokaci na kurewa, ko’ina a fadin kasar nan ba ka jin komai sai koke-kore da korafe-korafen rashin gamsuwa da halin da kasar ke ciki.

Fadar Gwamnatin Amurka da Majalisar Kasar sun yi mana hannunka-mai-sanda cewa ya kamata su kimtsa gidansu kafin ya ruguje. Haka ita ma Majalisar Ingila ta shaida mana. Ya zama dole su dubi maganganun da suke fada mana kuma mu yi tunanin abin da ka iya tasowa ta yadda za mu mai da hankali da irin wadannan shawarwari.

7 – Kalaman kiyayya tamkar dobarar daji ne

Idan aka yi turnuku fa ba ka da mai iya tsaida kalaman kiyayya da barkewar mummunan rikici. Kalaman kiyayya na kabilanci wutar kaikayi ce. Za ta rika ruruwa daga kasa, a karshe sai ta yiwo sama tana ci, ta yadda babu mai iya kashe ta, har sai ta yi barna. Idan kunne ya ji, to jiki ya tsira.

Tun bayan kashe ’yar Shugaban Kungiyar Afenifere, kusan sauran yankunan kasar nan sun harzuka, suna cewa abin ya ishe su haka nan fa! Duk lokacin da aka ci gaba da rashin maida hankali ga masu koke-koke, to kasar nan ce za ta ji a jikinta. Ni dai ina sanar da kai Shugaban Kasa kuma Babban Kwamandan Askarawan Najeriya cewa na damu kwarai da wadannan munanan bala’o’i da za a iya kauce musu.

8 – Sakin ragama da akalar Najeriya a hannun ’yan bindiga wadanda jama’a ke zargin cewa Fulani ne, sai kuma Boko Haram.

9 – Tsoron kada bala’in kashe-kashen ramuwar gayya ya barke a kan Fulani, ta yadda za mu fada irin bala’in da kasar Rwanda ta taba samun kanta a ciki. Babu wanda ya taba amanna cewa hakan za ta iya faruwa a Rwanda, amma ga shi kuma hakan ta faru.

10 – Tsoron kada irin wadannan kashe-kashe su koma a kan sauran wasu kabilun kasar nan tsakaninsu da wasu kabilu. Hakan na iya faruwa ta hanyar watsa jita-jita, fargaba, tsoro, barazana da kuma kisan daukar fansa da ka iya barkewa zuwa kisan kiyashi

11 – Fargabar barkewar yamutsi daga wani sashe na kasar nan da ka iya watsuwa zuwa sauran sassan kasar nan cikin kankaein lokaci, wanda a karshe zai iya kai ga raba kasar nan.

Saboda haka ya faru a Yugoslabia ba da dadewa ba. Idan ba mu tashi tsaye ba, to daya ko duka daga cikin wadannan bala’o’in ka iya faruwa. Dole mu tashi da addu’a tare da daukar matakin da ya dace a lokaci guda.

Wannan yunkuri kuwa Shugaban Kasa ne zai iya fara yin sa. Amma kuma ba zai iya cin nasara shi kadai ba, sai ya samu mataimaka. Masu iya magana na cewa idan kana cikin washin addarka, sai mahaukaci ya biyo ta bayanka, ya fizge wukar daga hannunka, to kana bukatar taimakon jama’a da za su hadu domin a karbe addar a hannun mahaukacim, ba tare da an ji wa wani rauni ba.

Ina fatan Buhari zai nazarci sakona da idon basira kada ’yan ba-ni-na-iya su ce masa martani ya kamata a yi wa Obasanjo kuma za mu iya, ba fage ba ne na sa-in-sa iya gaskiya na hakaito masa.

Buhari ga Obasanjo: Ba ka da kishin kasa

Sai dai a wani martani kan wasikar a karon farko Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana abin da Obasanjo ya yi da rashin kishin kasa. Buhari dai a baya bai tanka wa wasikun da Obasanjo ya aike masa, sai dai a lokacin da Shugaba Buhari yake jawabi ga shugabannin Kungiyar Yakin Neman Zabensa (BCO) a ranar Talatar da ta gabata a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, ya ce, “wadanda suke sukar gwamnati kan ‘matsalolin tsaron da ta gada’ a kasar nan ba masu kishin kasa ba ne.

Duk da cewa Buhari bai ambaci sunan Obasanjo ba, ya tabbatar da cewa kowace kasa a duniya tana fuskantar matsalar tsaro, inda ya ce, ayyukan ’yan bindiga da sace mutane ana garkuwa da su ana yin su a sassan duniya.

Wasikar Obasanjo na iya janyo fitina a Najeriya – Tanko Yakasai

Daya daga cikin Dattawan Arewa Alhaji Tanko Yakasai ya ce irin wadannan wasiku da Obasanjo ya saba fitarwa dabi’arsa ce ta rashin kishin kasa. Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana a ranar Talata a Kano cewa wannan wasika da Obasanjo ya rubuta wa Shugaba Buhari tana iya jawo tashin hankali a kasar nan.

Yace son kai ne yake sa Obasanjo wannan rubutu. “Aikin da Janar Obasanjo yake yi, ba komai b ane sai kokarin kawo tashin hankali a kasar nan da irin wadannan kalamai da sako na kiyayya suke yawo,” inji Yakasai.

A cewar Yakasai, irin wannan wasika da Obasanjo ya rubuta ne ta jawo masa shiga gidan yari a lokacin Janar Sani Abacha.

Alhaji Yakasai ya fahimci cewa manyan sojojin kasar nan kullum suna cikin fada ne da junansu ko da kuwa sun yi ritaya. Dattijon ya ce ba wannan ba ne farau wajen Obasanjo, ya yi wannan lokacin Janar Ibrahim Babangida, haka lokacin mulkin Sani Abacha har aka zarge sa da shirin kifar da gwamnati. Yakasai ya ce har yau wadannan wasiku suna nan.

Yakasai ya ce: “Ban ga kishin kasa a wasikun da Janar Obasanjo ke rubutawa ba.Hasali ma wasikun da ya rubuta wa dukkan shugabanin kasa na soja da farar hula ba don kishin kasa ya yi su ba. Domin abin da na sani game da siyasar Najeriya, manyan sojoji kullum suna fada da juna ne ya alla suna cikin aiki ne ko sun yi ritaya. Don haka ta wannan bangare duk wasikan da Janar Obasanjo ke rubutawa ga duk wani jami’in soja da ya mulki kasar nan ko shugaban siyasa babu kishin kasa a ciki.”

Ya ce wannan dabi’a ta rubuta wasikun rashin kishin kasa sun zame jiki ga Janar Obasanjo. Ya ce in ban da abu daya duk abin da ya fada an yi magana kansu, “Sabon abu da ya kawo shi ne na neman a kira taron kasa, wanda ban amince da shi ba,” inji shi.

Share