✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasu abubuwa game da Kobe Bryant

Yana dan shekara 17 ya fara buga a NBA wasa Shekara 20 yana buga wa Kungiyar Kwallon Kwando ta Lakers Sau biyu yana cin gasar…

  • Yana dan shekara 17 ya fara buga a NBA wasa
  • Shekara 20 yana buga wa Kungiyar Kwallon Kwando ta Lakers
  • Sau biyu yana cin gasar Olympic
  • Shi yake koya wa ’yarsa, Gianna kwallon Kwando

A karshen makon jiya ne fitaccen dan wasan Kwallon Kwandon nan na Duniya Kobe Bean Bryant ya rasu bayan da wani jirgin samansa mai saukar ungulu ya yi hadari da shi a Calabasas da ke Jihar Kalifoniya ta kasar Amurka. Bryant wanda kasar dan Amurka ne ya rasu ne a hadarin tare ’yarsa mai suna Gianna ’yar shekaru 14 da kuma wadansu mutum takwas.

Kobe ya shafe shekara ashirin yana buga wa Kungiyar Kwallon Kwando ta Lakers wasa da kuma Hukumar Wasan Kwallon Kwando ta Amurka, inda kwarewarsa wajen jefa kwallo a raga ta sa ya kasance daya daga cikin shahararrun ’yan wasan Kwallon Kwando da duniya ba za ta manta da su ba. Kobe dan wasa ne mai hikima wanda ya kasance dan wasa mafi karbar lambobin yabo a Amurka, dogo ne mai tsawon mita 1.98.

Ya ci wa kasar Amurka kyautukan lambobin zinare a gasar wasannin Olympic ta Duniya har sau biyu, wato a shekarar 2008 da kuma 2012.

An haifi Kobe Bryant a ranar 23 ga Agustan 1978 a garin Philadelphia na Jihar Pennsylbania ta kasar Amurka. Ya fara buga kwallon kwando a ajin kwararru na NBA na kasar Amurka yana dan shekara 17. Ya rasu yana da shekara 41 a duniya.

Bryant ya auri wata mata mai suna Banessa a shekarar 2001. Suna da ’ya’ya hudu; Natalia wacce suka haifa a shekarar 2003 da Gianna wacce suka haifa a 2006 da Bianka wacce suka haifa  a 2016, sai kuma  Capri wacce suka haifa bara.

An sa ran shi da ’yarsa Gianna su halarci cibiyar wasanni ta Mamba Sports Academy da ke Thousand Oaks domin halartar wani wasan kwallon kwando da aka shirya za a yi a ranar Lahadin da ta gabata, inda ake sa ran shi ne zai horar da kungiyar da ’yarsa take buga wa wasa.

Bryant ya fadi cewa ya jima ba ya kallon wasan kwallon kwando tun bayan da ya yi murabus a 2018, ya lashe kyautar yabo to, amma ganin yadda ’yarsa take son yin wasan kwallon kwando ya sanya ya amince ya horar da kungiyar.