Da Dumi Dumi

Wasu daga cikin rahotannin marigayi Bashir Musa Liman

Marigayi Bashir Musa Liman
Marigayi Bashir Musa Liman

A ranar Asabar, jajibirin Babbar Sallah ce muka hadu da labarin rasuwar wakilin Aminiya a Jos, Bashir Musa Liman, wanda ya kwanta dama a sanadiyar hadarin mota da ya rutsa da shi a kusa da garin Ningi a kan hanyarsa ta zuwa gida Jama’are domin bikin Sallah.

Rasuwar Bashir Liman ta firgita duk wadanda suka san shi  da kuma ’yan jarida baki daya, kasancewar duk mai mu’amala da jaridun Trust, musamman Aminiya da Daily Trust  Sartuday zai shiga dimuwa kasancewa Bashir Liman sanannen suna ne.

A cikin wani sakonsa kusan na karshe-karshe a manhajar WatsApp, ya tura wa abokansa sakon murya inda yake cewa, “Sunana Bashir Musa Liman. Zan ba ku shawara kyauta. Ba abin da ke kasancewa na dindindin a duniyar nan. Kudi, mulki da kyau, duk za su gushe. Aikinka ne kawai za su kasance. Idan ka yi aiki mai kyau za ka gani, idan kuma ka yi na banza ma za ka gani. Aiki mai kyau zai kai ke Aljanna, na banza kuma ya kai ka wuta. Ka gyara yau dinka da ayyuka masu kyau, domin gobenka ya yi kyau, ka ji dadi!”

Tarihinsa a takaice:

Cikakken sunansa Bashir Musa Liman. An haife shi a garin Jama’are a Jihar Bauchi. Ya yi makarantar firamare a garin Jama’are. Ya fara karamar sakandare a Bauchi, kafin ya wuce zuwa Kwalejin Gwamnati da ke Toro a Jihar Bauchi, inda a nan ya kammala sakandare dinsa. Daga nan ya wuce zuwa Jami’ar Maiduguri, inda ya karanci bincike kan duwatsu da albarkatun kasa (Geology), sannan ya yi hidimar kasa a Jihar Delta.

ADVERTISEMENT

Bayan kammala hidimar kasa sai ya kama aiki da Kamfanin Media Trust, mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya a hedkwatarsa da ke Abuja..

Kuma yana aiki a kamfani ne ya samu aiki da Gwamnatin Tarayya a Hukumar Binciken Duwatsu da Albarkatun Kasa inda aka tura shi Jihar Filato.

Sakamakon kwazonsa ya sa Kamfanin Media Trust ya ba shi aiki a matsayin dan jarida mai zaman kansa (freelancer) don ya rika aiko da rahotonni daga sabon wurin aikinsa wato Jos.

Bashir ya kasance mutum ne jajirtacce, mai hikima da fasaha wajen aiki.

Ya yi rahotanni masu yawa da muhimmanci musamman a bangaren masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, inda za a iya cewa ya san duk ’yan Kannywood, domin duk lokacin da aka bukaci wani abu, cikin sauri da sauki Bashir yake tattarowa.

Sannan ya yi manyan rahotanni game da al’amuran da suka shafi Jihar Filato, cikin kwarewa ba tare da nuna bambanci ko kabilanci ba, wanda hakan ya sa Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya aika da sakon ta’aziyar rasuwarsa.

Kwanakin baya ya bude Mujallar Tauraruwa. inda yake tattaunawa da ’yan fim a bidiyo.

Wasu daga cikin rahotanninsa da suka yi tasiri sosai:

Rikicin Ali da Zango: Asalinsa da yadda karamar magana ta zama babba, wanda aka buga a Aminiya a ranar 18 ga watan Afrilun  2019.

Zaben 2019: ’Yan fim sun rabu kan Buhari da Atiku, wanda shi ne  babban labarin jaridar Aminiya a ranar 9 ga Nuwamba, bara

Inteesar el-Fallatah: ’Yar fim da ta ajiye aktin ta koma bayan kyamara, wanda aka buga a ranar 27 ga watan Yunin 2019

‘Make Room:’ Fim din Hausa da aka kasafta Naira miliyan 300, wanda aka buga a shafin Dandalin Nishadi na ranar 27 ga watan Oktoba, shekarar 2017

Burina in zama Furodusan da zai yi fice a duniya – Maishadda, wanda aka buga a ranar 20 ga watan Yuni, 2019

Kazafi aka yi mini, ban ce Gabon da Maryam karuwai ne ba – Tanimu Akawu

Rahotonsa na karshe ke nan a Aminiya wanda aka buga a shafin  ranar 2 ga watan Agusta, shekarar 2019

Sharhin Fim din ‘MATAN GIDA’ Na Daya Da na Biyu, wanda aka buga a ranar 18 ga watan Fabrailu, shekarar 2013

An kirkiro tashe don gyara tarbiyyar rayuwar Bahaushe ne – Farfesa Lawan Danladi Yalwa, wanda aka buga a shafin Adabi a ranar 10 ga Agustan shekarar 2012

Inda aka kwana a batun sulhunta Gabon da Amal, wanda aka buga ranar 15 ga watan Mayu, 2019.

Dalilin da ya sa na fara fim din Hausa-Nkem Owoh, wanda aka buga a ranar 31 ga watan Oktoba, shekarar 2013 

Why Kannywood deserbes ministerial slot in Buhari’s gobt. – Abdul Amart, wanda aka buga a Daily Trust Saturday, ranar 17 ga Yuni, 2019

EDCLUSIBE: Kannywood: Hadiza Gabon denies police arrest report, says “I didn’t kneel to beg Nabraska”, wanda aka buga a ranar 21 ga watan Mayu, 2019

Kannywood: Zango’s sidth marriage postponed until after Sallah,wanda aka buga a ranar 24 ga watan Afrilu, shekarar 2019

Kannywood’s Zango writes open letter to ‘haters,’ wanda aka buga a ranar 13 ga  Nuwamba, shekarar 2017

Kannywood’s Zango flaunts N23m Wrangler Jeep, wanda aka buga a ranar 3 ga watan Yuli, 2019

Kannywood’s Nafisa blasts Buhari ober Zamfara killings, wanda aka buga a ranar 4 ga watan Afrilu, shekarar 2019

Kannywood: APC Musicians accuse Buhari’s Music Director, Rarara of corruption, wanda aka buga a ranar 26 ga watan Yuni, shekarar 2019

Kannywood star ‘dumps’ Buhari for Atiku, wanda aka buga a ranar 7 ga Fabrailu, 2019

 ‘How prank call led to BBC report which accused me of diborcing my wife’, wanda aka buga a ranar 2 ga Fabrailu, 2019

‘Make Room’: The Hausa film targeting an Oscar, wanda aka buga a ranar 2 ga watan Satumban 2017

I wouldn’t mind acting in an Igbo mobie – Auwal Bala

Rahotonsa na karshe ke nan a Daily Trust Saturday da ke fitowa duk ranar wanda aka buga a ranar Asabar din d da ya rasu.

Hakika Bashir Liman ya bar babban gibi mai wuyar cikewa musamman a fannin aikin jarida da kuma labaran masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood.  Wannan ya sa a watan jiya Kamfanin Media Trust ya aike masa da wasikar yabo tare da wani dan hasafi don yaba kwazonsa.

Allah Ya jikansa da rahama

 

Share