✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasu kamfanoni ne ke cin moriyar rufe iyakokin Najeriya a maimakon manoma – Dan Kasuwa

A farkon makon jiya ne taron masana daga kasasashen duniya da aka yi a Abuja ya goyi bayan Najeriya ta ci gaba da rufe kan…

A farkon makon jiya ne taron masana daga kasasashen duniya da aka yi a Abuja ya goyi bayan Najeriya ta ci gaba da rufe kan iyakokinta na lokaci mai tsawo muddin tana son cimma burinta na tsayawa da kafafunta a bangaren abinci.

Taken taron na Abuja shi ne ‘Tunkarar sababbin kalubale da ke dubi kan ci gaban harkar noma a Afirka bayan shekara ta 2020.’ A daidai wannan lokaci ne kuma wani mai hada- hadar kasuwanci a Najeriya, Alhaji Babangida Musa ya ce bai goyi bayan ci gaba da rufe kan iyakokin ba domin hana shigo da shinkafa cikin kasa amma ya goyi bayan rufe kan iyakokin domin hana shigo da makamai da kwayoyi.

Da yake fadin hujjarsa a zantawar da Aminiya a Ibadan dan kasuwar cewa, ya yi “Abin bakin ciki ne ganin cewa, gwamnati tana kashe dimbin kudi tun daga shekarar 2015 da aka fara shirin noman shinkafa a cikin gida amma har yanzu shirin bai haifar da da mai ido ba, saboda wasu kamfanoni masu shiga tsakani ke cin moriyar shirin su kadai maimakon manoma da al’ummar kasa.”

Ya ce “Har yanzu shinkafar da ake nomawa a cikin gida farashinta karuwa yake yi  maimakon ya yi kasa ta yadda talaka zai iya saya.”

Saboda haka yake ganin bai dace gwamnati ta rufe kan iyakokinta domin hana shigo da kayan abinci musamman shinkafa ba, domin Allah bai wadata Najeriya da kasar noman shinkafa ba amma akwai kasar noman dawa da masara isasshe. Saboda haka ya kamata gwamnati ta yi amfani da wannan kudi wajen habaka noman dawa da masara da suka samu karbuwa daga nau’in kasar noma.

Ya ce wani muhimmin abu shi ne, “Najeriya ba za ta iya noma shinkafar da za ta iya ciyar da miliyoyin jama’arta ba dalilin wasu matsaloli kamar bayar da tallafi ga manoma cikin kurarren lokaci da kasa samar da tsayayyen farashi mai rahusa da manoma za su samu ribar da za ta karfafa musu gwiwar rungumar noman shinkafa a nan gaba. Kuma muddin aka kyale irin wadannan kamfanoni suka ci gaba da shiga tsakani to hasara kawai za su janyo wa masu noman shinkafa su yi watsi da wannan sana’a nan gaba,” inji shi.

Alhaji Babangida Musa, ya ce “Masu fataucin kayan abinci a ciki da wajen Najeriya sun yi hasarar miliyoyin kudade na nau’in kayan abinci kamar doya da tumatir da dabino da aya da makamantansu wadanda suka lalace dalilin rufe kan iyakokin da ya zo musu ba zata. Bai kamata a hana shigowa da fitar da irin wadannan kayan abinci ba. Ya kamata gwamnati ta yi nazari sosai kan wadannan matakai da suka shafi huldar kasuwanci tsakanin kasa da kasa. Kuma yana da kyau a bude kan iyakar Najeriya da makwabtan kasashe masu sha’awar shigo da shinkafa daga ketare su ci gaba da gudanar da sana’arsu suna biyan harajin fito ga gwamnati. Kuma gwamnatin ta sa ido sosai a kan masu yi mata zagon kasa ta fannin shigo da makamai da kwayoyi.”