Aminiya

Wasu Matasan Fulani sun tuba daga miyagun ayyuka a Jihar Oyo

Shugaban Kungiyar Miyetti Allah a Jihar Oyo Alhaji Yakubu Bello ya ce, yanzu haka akwai wasu matasa masu yawa a tare da su da suka tuba daga miyagun ayyukan da suke yi kuma sun yi rantsuwar daina aikata miyagun ayyuka da suke yi.

Wadannan matasa sun yi rantsuwar ne a gaban shugabannin Kungiyar Miyetti Allah ta kasa a lokacin da suka kawo ziyara ta musamman a Jihar Oyo.’

ADVERTISEMENT

Alhaji Yakubu Bello ya bayyana hakan ne a wajen taron masu ruwa da tsaki a kan tsaro da Rundunar ‘Yan Sanda shiyya ta 11 da ke kula da Jihohin Osun da Oyo da Ondo ta shirya a Ibadan. ‘Wannan yana daga cikin irin gudunmawar da Kungiyar Miyetti Allah take bayarwa ne domin kyautata tsaron lafiyar al’umma musamman da yake Jami’an tsaro na soja da ‘yan sanda su kadai ba za su iya ba.’ In ji Shugaban Kungiyar ta Miyetti Allah wanda ya ci gaba da shaidawa taron cewa, ‘matasan da suka yi rantsuwar daina aikata miyagun ayyukan yanzu suna nan cikin jama’a da mahukunta suke amfani da su ta fannoni daban daban.’ Ya yi kira ga sauran jama’ar kasa kowa ya fito da irin ta shi gudunmawar da za ta taimaka wajen murkushe miyagun ayyuka a Najeriya.

Tun da farko cikin jawabin maraba Kwamishinan ‘Yan sanda na Jihar Oyo Mista Shina Olukolu ya roki Gwamnatin Jihar Oyo ne ta kara rubanya tallafin da ta saba bayarwa ga Rundunar musamman kayan aiki da suka hada da motoci wanda su ne manyan matsalolin da suka dabaibaye Rundunar a yanzu. A daidai wannan lokaci ne Mai ba Gwamna shawara a kan harkokin tsaro Mista Segun Abolanrinwa ya tabbatar wa taron cewa Gwamna Abiola Ajimobi ya aiko shi da sakon cewa ‘kafin gwamnati ta mikawa sabuwar gwamnati karagar mulki a karshen watan da muke ciki na Mayu, za ta yi duk abun da take iyawa wajen ganin ta share hawayen rundunar ‘Yan Sandan ta fannin wadata su da kayan aiki da ta nema domin kyautata tsaron lafiyar al’umma da samar da zama lafiya a Jihar Oyo.

ADVERTISEMENT

Cikin jawabinsa Shugaban Taron, Mataimakin Sufeto-Janara (AIG) Leye Oyebade ya nuna matukar farin cikinsa da irin yadda kowane bangare na masu ruwa da tsaki suka amsa goron gayyatar zuwa wajen wannan taro. Ya ce, daya daga cikin amfanin shirya irin wannan taro shi ne zama a teburin tattaunawa tsakanin kowane bangare na jama’ar a kan yadda za a samo hanyar dakile miyagun ayyuka.

Ya yi kira ga sarakunan gargajiya da malaman addinai da kungiyoyin direbobin motocin sufuri da kungiyoyin manoma da makiyaya da kungiyoyin ‘yan kasuwa wadanda kowanne ya aika da wakilai zuwa wajen taron da su tabbatar da bayar da gudunmawarsu ga harkokin tsaro a Najeriya.