✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasu tsoffin shugabannin Najeriya ba su halarci rantsar da Buhari ba

A yau Laraba da ake rantsar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari karo na biyu wasu tsoffin shugabannin Najeriya, kamar su Ibrahim Badamasi Babangida da Olusegun…

A yau Laraba da ake rantsar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari karo na biyu wasu tsoffin shugabannin Najeriya, kamar su Ibrahim Badamasi Babangida da Olusegun Obasanjo ba su halarcin bikin rantsar da shugaban ba da aka yi a dandalin Eagle Square, da ke Abuja.

Tsohon shugaban Najeriya Janar Yakubu Gowon, da kuma shugaban rikon gwamnati Cif Ernest Shonekan
ne suka halarci bikin rantsarwar.

Mukaddashin Alkalin Alkalan Najeriya (CJN), Mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad, ne ya rantsar da shugaba Buhari da misalin karfe na safe 10:37.  Buhari ya samu rakiyar matarsa Aisha lokacin rantsuwar.