✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata 9 ba a biya mu tallafinmu na wata-wata ba – Nakasassun Sakkwato

Jihar Sakkwato kamar sauran jihiho a Najeriya sun yi bikin ranar nakasassu, sai dai bikin bai samar da nasarar da ake bukata ba, domin da…

Jihar Sakkwato kamar sauran jihiho a Najeriya sun yi bikin ranar nakasassu, sai dai bikin bai samar da nasarar da ake bukata ba, domin da yawan nakasassun sun kauracewa bikin da Gwamnatin Jihar Sakkwato ta shirya saboda korafin da suke yi gwamnati ta yi watsi da su, kuma ba sa more romon dimokuradiyya, inda suka ce a yanzu suna bin Gwamnatin Jihar Sakkwato bashin wata tara na tallafin da ake ba su duk wata na Naira dubu 6,500.

A lokacin da mai girma gwamnan Aminu Waziri Tambuwal ya fara jan ragamar mulkin Jihar Sakkwato ya yi taro da nakasassun, inda ya yi alkawarin cewa zai jawo su jiki, kuma zai taimaka musu dari bisa dari, kuma zai sa su cikin gwamnatinsa, bayan daukar karatun yaransu.

Rashin cika wannan alkawarin ne ya sa suke korafi wanda har ya sa wasu kauracewa taron, kuma abin da ya sa wasu nakasassun suk koma harkar baransu a jihar da makwabtan jihohi.

Malam Amadu Gurmu Sifawa, Shugaban Kungiyar Nakasassu Karamar Hukumar Bodinga a zantawarsa da Aminiya ya ce, “rayuwa duk inda aka samu nasara akwai matsala, muna kira ga gwamnati da ta cigaba da ba mu tallafinmu na wata-wata da ake ba mu, muna jiran wannan watan.

“Muna son gwamnati ta shigo ta tallafa wa nakasassu domin akwai wadanda suka kammala karatu ba su da aikin yi, akwai masu son sana’a ba jari, ga yaranmu da aka dauki sunayensu domin ba su tallafin karatu shi ma har yanzu ba a yi ba.”