✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata Hajiya daga Najeriya ta rasu a Saudiyya

Hukumar Kula da Al’amuran Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta ce, an sake samun wata Hajiya da ta rasu wadda ‘yar jihar Sakkwato ce. Shugaban…

Hukumar Kula da Al’amuran Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta ce, an sake samun wata Hajiya da ta rasu wadda ‘yar jihar Sakkwato ce.

Shugaban sashen lafiya na Hukumar NAHCON Dakta Hamidu Liman, ne ya sanar da hakan ga manema labarai a birnin Madina da ke Kasar Saudiyya.

Dakta Hamidu, ya ce marigayar ta rasu ne bayan jinyar kwana hudu a asibitin Al-Ansar, ya kuma Hajiyar dai ba tada lafiya tun kafin zuwanta kasa mai tsarki, amma bayan zuwanta sai rashin lafiyan ya yi tsanani.

An yi jana’izarta a birnin Madina ranar Juma’ar da ta gabata.