✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata mace ta laka wa matashi satar waya ta sa an kashe shi an jefa a ruwa

Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas ta kama wata mata wadda ake zargi da laka wa wani matashi satar waya ta kuma yiwo hayar wadansu matasa…

Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas ta kama wata mata wadda ake zargi da laka wa wani matashi satar waya ta kuma yiwo hayar wadansu matasa suka yi ta dukansa har sai da sannan suka jefa shi a cikin kogi .

Lamarin ya faru ne a Unguwar Abidjan da ke daura da Kogin Legas.

’Yar uwan matashin mai suna Olamide Omolegbe ta ce matashin ya kai cajin wayarsa ce a  wani shago a daidai lokacin da matar ita ma ta sanya cajin wayarta a wajan, kuma bayan da ya koma gida sai matar ta zo tana cigiyar wayarta inda ta ce matashin mai shekara  22  ne ya dauke wayar, kuma nan take ta kira wadansu ’yan daba wadanda suka kamo matashin suka yi masa tsirara suna zagayawa da shi cikin ugunwar suka yi ta jibgarsa har ya mutu kafin su jefa gawarsa a kogin.

Daga bisa ni an gano wayar matar a hannun danta lamarin da ya sanya dattawan unguwar suka shigar da kara a ofishin ’yan sandan Langbasa.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas, DSP Bala Elkana ya shaida wa Aminiya cewa rundunar ta kama mutum hudu da ake zargi da kisan matashin da matar mai suna Bolanle Muhammed wacce da ake zargi da yi wa matashin sharrin satar wayarta inda ta yi hayar mutum hudu suka hallaka shi suka kuma jefar da gawarsa a ruwa. Ya ce Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Alhaji Zubairu Mu’azu ya ba da umarnin a ci gaba da bincike kafin a gurfanar da su a kotu don fuskanci hukunci yayin da ’yan sandan suka ciro gawar matashin daga kogi aka kai ta dakin ajiyar gawar na Asibitin Mainland a Legas.