✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata mata ta bace tare da yara 2

Akarshen makon jiya ne wata mata da ba a san ko wace ce ba ta bi ta Layin Amadi a birnin Fatakwal na Jihar Ribas…

Akarshen makon jiya ne wata mata da ba a san ko wace ce ba ta bi ta Layin Amadi a birnin Fatakwal na Jihar Ribas lokacin wadansu yara kanana suke wasa inda aka yi zargin bayan ta wuce yaran ne aka nemi yaran biyu kasa ko sama ba a gansu ba.

Yaran biyu kamar yadda wakilin Aminiya ya samo sunayensu su ne, Goodnews Friday da ’yar shekara daya mai suna Prosper Solomon.

Da yake yi wa manema labarai bayani kan yadda dansa ya bata mahaifin Goodnews mai suna Nelson Friday, ya ce “Ba mu fargaba sai da muka dawo daga coci misalin karfe biyu na rana bayan da muka shiga gida ba mu ga yaran ba.”

Ya ce, an bar yaran suna wasa a kofar gida ne ashe ba wani wanda ya san cewa, wata mace ta yaudari yaran ta tafi da su domin mutanen unguwa babu wanda ya yi tsammani ba ’yar uwa ko ’yar unguwar ba ce.

Bayanan da wakilinmu ya kalato daga makwabta sun nuna cewa, wata mata ce ta gamu da wadda ta sace yaran, sai jikinta ya ba ta ta ankarar da jama’a.

Wani makwabcin Nelso Friday, da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce, “Ranar Lahadi mun samu labarin cewa ga wata mata can ta wuce mana da yara shi ne muka baro coci muka dawo gida.”

Iyayen yaran sun ce, bayan  shaida musu sace yaran nasu biyu da ake zargin wata mata ta yi sun je karamin ofishin ’yan sanda na unguwar, amma a cewarsu babu wani mataki kwakkwara da suka dauka game da lamarin abin da ya harzuka su ke nan suka tafi ofishin ’yan sanda da ke Mil Daya suka kai rahoton, “Su kuma da muka je cewa suka yi babu wani abu mai kama da haka da aka kawo musu korafi,” inji makwabcin.

Wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Ribas, Nnamdi Omoni, inda ya ce ba ya gari don haka ba zai iya karar da komai ba game da lamarin.