✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata mata ta cire wa kishiyarta kunne da cizo

Wata mata ta yago kunnen kishiyarta da cizo a yayin fadan da ya kaure tsakaninsu a kan dan daya daga cikinsu. Kishiyoyin masu suna Rabi…

Wata mata ta yago kunnen kishiyarta da cizo a yayin fadan da ya kaure tsakaninsu a kan dan daya daga cikinsu.

Kishiyoyin masu suna Rabi da Zubaida sun yi ta ba wa hammata iska ne a gidan mijinsu da ake kira Dan Borno, a Unguwar Zai, da ke karamar hukumar Dutse a jihar Jigawa.

Fada ya fara kaurewa tsakanin Zubaida da Rabi har suka yi ta bugun juna ne bayan dan Rabi ya zuba ruwa a cikin tankin injin din Zubaida, saboda ta zage shi.

Ana cikin dauki ba dadin ne Zubaida, wadda aka zuba wa injinta ruwa, ta gantsara wa Rabi cizo a kunne, sai da ta yago rabin kunnen.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar jigawa, SP Abdu Jinjiri, ya ce Zubaida da Rabi sun amsa tambayoyi kafin a ba da belinsu a caji ofis na karamar hukumar Dutse.

SP Jinjiri ya kara da cewa da zarar ’yan sanda sun kammala bincike a kan al’amarin za a gurfanar da matan a gaban kotu domin su girbi abin da suka shuka.

Wani makwabcin gidan Dan Borno a Unguwar Zai ya shaida wa Aminiya cewa Zubaida da Rabi sun dade suna zaman doya da manja da fada a kan ’ya’ya, har ta kai ’ya’yan daya ba sa zuwa kofar dakin daya saboda tsananin kishi.

A wasu lokauta akan samu matan da kan jikkata abokan zamansu ko ma su yi yunkurin hallaka su ba don komai ba sai don tsananin kishi.