✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata mata ta damfari coci Naira miliyan 100

Wata mata mai suna Iwuagwu Onyinyechi mai shekara 39 ta shiga hannun ’yan sanda a Jihar Ogun bayan da aka zarge ta da damfarar wani…

Wata mata mai suna Iwuagwu Onyinyechi mai shekara 39 ta shiga hannun ’yan sanda a Jihar Ogun bayan da aka zarge ta da damfarar wani coci kudi wuri na gugar wuri har Naira miliyan 100.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi ya shaida wa Aminiya cewa matar ta yaudari jami’an cocin ne wadanda ke da sashin juya kudi da ake kira da MIA Enterprises inda ta ce za ta taimake su ta samar musu da makudan kudi da za su yi amfani da su a ayyukansu na taimakon jama’a, “Rundunarmu ta kama matar da ake zargi ne bayan takardar koke da lauyan cocin Barista Godswill Ojakobo ya shigar a offishin Kwamishinan ’Yan sandan Jiha inda ya shaida mana cewa matar ta damfari cocin Naira miliyan 100,” inji shi.

Ya ce matar da ake zargin ta zo da takardun shAIdar cinikayya (LPO)  da ta ce na wani kamfani ne da aka ba ta damar sayarwa, inda ta buKaci cocin ya biya kudin kuma suka tura mata Naira miliyan 33 da dubu 118 ta Intanet kafin daga baya ta sake komowa da wasu takardu inda a karo na biyu jami’an cocin suka tura mata Naira miliyan 77, bayan da suka tura mata kudin a karo na biyu ne ba su sake jin doriyarta ba tun a watan Satumban bara. Kuma da suka binciki takardun da ta ba su sai suka gano cewa takardu ne na bogi,  lamarin da ya sanya su rubuta takardar koken.

Abimbola Oyeyemi ya ce bayan da rundunar ta bibiyin takardar koken ne Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ahmed Iliyasu ya bai wa sashin binciken kwakawaf na rundunar umarni bin bahasi inda suka binciko matar a ranar 21 ga watan Janairun da ya gabata, bayan binciken da aka yi mata ne ta amince da zargin inda ta ce ta yi amfani da takardun bogi wajen damfarar cocin.

Kwamishinan ’Yan sandan ya ba da umarnin a gurfanar da wacce ake zargi a gaban kotu da zarar an kammala bincike