✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata ta damfari Osaze Odemwingie Naira miliyan 19 a Ingila

Yanzu haka wata kotu a Birtaniya tana tuhumar wata mata mai suna Claire Duke, mai kimanin shekara 38 da laifin damfarar wadansu ’yan kwallo a…

Osaze OdemwigieYanzu haka wata kotu a Birtaniya tana tuhumar wata mata mai suna Claire Duke, mai kimanin shekara 38 da laifin damfarar wadansu ’yan kwallo a Ingila ciki har da dan asalin Najeriya Osaze Odemwingie kamar yadda kafar yada labarai ta naij.com ta kalato.
An ce matar wacce take taimakawa ’yan kwallon ta hanyoyin daban-daban da ake wa lakabi da Turanci (Consultant) a bangaren bayar da shawarwari da kuma aika sakonni ta hannunta, ta yi amfani da damar ce wajen zaftare kudaden da suke ba ta wajen aika wa iyalansu ko kuma yin ajiya a banki.
Odemwingie da yanzu haka yake buga kwallo a kulob din Cardiff City a Ingila matar ta damfare shi Fam dubu 70 kwatankwacin Naira miliyan 19 ne a tsakanin shekara guda.
A ranar Larabar da ta wuce ne dai aka gabatar da matar a kotu inda ake tuhumarta da laifuffuka biyar ciki har da na zamba cikin aminci.
Kotu ta shaida mata cewa a tsakanin watan 1 ga watan Satumbar bara zuwa 10 ga Yulin bana, ana tuhumarta da laifin yin sama da fadi da kudin wadansu ’yan kwallo da suka kai Fam dubu 71 da 106 kwatankwacin Naira miliyan 19.
An ce matar baya ga damfarar Osazae makudan kudi, akwai lokacin da ta yi amfani da katin cire kudinsa na ATM ta yi awon gaba da Fam dubu 15 kwatankwacin Naira miliyan hudu ba tare da izininsa ba.
Yanzu haka kotun ta dage sauraron karar zuwa wani lokaci kuma ta bayar da umarnin a cigaba da tsare matar a gidan kaso har sai an kammala bincike.
Shi dai Osaze Odemwingie haifaffen Rasha ne amma mahaifinsa dan Najeriya ne da ke zaune a Ingila.  Ya yi wa kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles wasa kafin daga bisani su samu sabani da koci Stephen Keshi inda kocin ya daina gayyatarsa don buga wa kungiyar wasa.  Ya buga kwallo a kulob din Bendel Insurance a tsakanin shekarar 2000 zuwa 2002 kafin ya koma Rasha inda ya yi kwallo a kulob din Lille OSC sannan ya canza sheka zuwa Lokomotib ta Mosko daga nan ya koma Ingila a shekarar 2010 inda ya koma kulob din West Brom da ke buga kwallo a gasar rukunin Premier ta Ingila.  A farkon shekarar nan ce ya koma kulob din Cardif City da ke Ingila inda yanzu haka yake buga kwallo.
Ya yi wa kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles kwallo kafin su samu sabani da Koci Stephen Keshi, inda kocin ya daina gayyatarsa.  Amma rahotannin da ke fitowa koci Stephen Keshi ya fara yunkurin sake gayyatar Osaze don tafiya da shi gasar cin kofin duniya da za a yi a shekara mai zuwa a kasar Brazil.