Da Dumi Dumi

Watakila a dage gasar Firimiya ta Ingila  gaba daya saboda Kurona

Watakila a dage gasar Firimiya ta Ingila

Wasu rahotannin da ba a tantance ba sun ce akwai yiwuwar a dage gasar Firimiya ta Ingila ta bana gaba daya saboda matsalar cutar Kurona.

Idan ba a manta ba a ranar Juma’ar da ta wuce Hukumar Shirya Gasar ta  dage gasar zuwa ranar 4 ga Afrilu ganin yadda cutar take ci gaba da yaduwa a sassan duniya ciki har da Ingila.

Rahotanni sun ce da wuya in za a iya ci gaba da gasar a ranar 4 ga Afrilun ganin yadda  cutar take ci gaba da ta’azzara.

Hakan ya sa wadansu ke hasashen za a iya dage gasar ta bana kwata-kwata, inda  za a iya mika kofin kai-tsaye ga kulob din Liberpool da ke saman teburin gasar da maki 82 bayan ya bayar da tazarar maki 25 kuma ana saura wasa 9 a kammala gasar, sai dai wadansu na ganin hakan ba mai yiwuwa   ba ne.

A ra’ayin tsohon Kyaftin din Newcastle United na Ingila, Alan Shearer ya nuna ko an dage gasar bai dace a mika kofin ga kulob din Liberppool ba don komai zai iya faruwa a harkar kwallon kafa.

ADVERTISEMENT

Ya ce “Duk da abu ne mai wahala a iya kamo Liberpool ganin yadda ta bayar da tazara mai yawa amma komai zai iya faruwa a harkar kwallon kafa.”

Liberpool dai tana bukatar hada maki shida ne kafin ta lashe gasar kuma ana saura wasa 9 don haka bai dace a mika  mata kofin kai-tsaye ba ko da an dage gasar, inji Alan Shearer a wata hira da ya yi da manema labarai a ranar Talatar da ta wuce.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya