✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Watakila a dakatar Ronaldo shekara biyu

Rahotannin da ke fitowa daga Italiya sun ce akwai yiwuwar Hukumar Kwallon Kafa ta Kasar ta dakatar da shahararren dan kwallon Jubentus Cristiano Ronaldo na…

Rahotannin da ke fitowa daga Italiya sun ce akwai yiwuwar Hukumar Kwallon Kafa ta Kasar ta dakatar da shahararren dan kwallon Jubentus Cristiano Ronaldo na tsawon shekara biyu.

Dan kwallon zai iya fuskantar wannan hukunci ne bayan ya bar filin wasa a mintii na 87 a ranar Lahadin da ta wuce a wasan da kulob din Jubentus ya yi da na AC Milan a ranar Lahadin da ta gabata.

Ana gab da tafiya hutun rabin lokaci ne sai kocin Jubentus Sarri ya canja Ronaldo da Paulo Dybala kuma shigarsa ke da wuya ya zura kwallo daya tilo a ragar AC Milan inda aka tashi wasan 1-0.

Sai dai Ronaldo bai ji dadin canjin ba, abin da ya sa ya fusata kuma ya bar filin wasan a minti na 87.

A wata hira da gidan talabijin na Italiya ya yi da tsohon dan kwallon Italiya Antonio Cassano ya ce za a iya dakatar da Ronaldo tsawon shekara biyu a Italiya saboda laifi ne dan kwallo ya bar filin wasa kafin a tashi kamar yadda Hukumar Yaki da Shan Kwayoyi masu Kara Kuzari a tsakanin ’Yan wasa  (Anti-Doping Agency) ta nuna.

Masoya kwallon kafa sun zuba ido su ga yadda al’amarin zai kasance.