✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Watakila Kocin Super Eagles ya yi murabus

Rahotannin da ke fitowa daga Abuja sun nuna akwai yiwuwar kocin Super Eagles, Gernot Rohr zai jefar da kwallon mangwaro don ya huta da kuda. …

Rahotannin da ke fitowa daga Abuja sun nuna akwai yiwuwar kocin Super Eagles, Gernot Rohr zai jefar da kwallon mangwaro don ya huta da kuda.  Kocin ya fara tunanin ajiye aiki ne a matsayinsa na kocin kungiyar ganin yadda da yawa daga cikin magoya bayan kungiyar ba su gamsu da aikinsa ba.

Gernot Rohr mai shekara 66 xan asalin Jamus. ya taimaki Najeriya halartar Gasar Cin Kofin Duniya a bara sannan ya taimaki kasar nan wajen zama ta uku a Gasar Cin Kofin Afirka da aka yi a Masar.

Sai dai duk da waxannan nasarori da kocin ya samu, magoya bayan kungiyar ba su gamsu da yadda yake horar da ’yan kwallon Eagles ba. Hasali ma waxansu sun ce kocin yana tafiya da sa’a ce kawai maimakon kwarewa.

Kafar watsa labaran wasanni ta ESPN ta ruwaito a ranar Talatar da wuce cewa kocin ya gana da Shugaban Hukumar NFF, Mista Amaju Pinnick amma zuwa haxa wannan labari ba a san matakin da aka zartar ba game da batun yin murabus xin kocin daga Eagles.