✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Watakila Mourinho ya sake zama kocin Chelsea a karo na uku

Rahotanni da ke fitowa daga kulob din Chelsea da ke Ingila sun nuna akwai yiwuwar tsohon kocinsu Jose Mourinho ya sake horar da kulob din…

Rahotanni da ke fitowa daga kulob din Chelsea da ke Ingila sun nuna akwai yiwuwar tsohon kocinsu Jose Mourinho ya sake horar da kulob din a karo na uku a kaka mai zuwa.

A halin da ake ciki Mourinho yana daga cikin koci uku da kulob din yake zawarcinsu da zarar ya rabu da kocinsu na yanzu Maurizio Sarri, dan asalin Italiya.

Alamu sun nuna Sarri zai canja sheka ne zuwa kulob din Jubentus na Italiya duk da nasarar lashe kofin Europa ga Chelsea a watan jiya.  Kuma wannan shi ne babban kofin da ya taba lashewa tun bayan da ya kama harkar horarwa.

Idan Mourinho ya samu nasarar zama kocin Chelsea, wannan shi ne karo na uku da zai horar da kulob din kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Dan asalin Fotugal, Mourinho dai ya taba horar da Chelsea ne a tsakanin shekarar 2004 zuwa 2007 da kuma a 2013 zuwa 2015.  Ya horar da kulob da dama da suka hada da kulob din Real Madrid na Sifen da Inter Milan na Italiya da Chelsea da kuma Manchester United dukkaninsu a Ingila.