✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Watakila Samuel Eto’o ya koma kulob din Chelsea

Shahararren dan kwallon Kamaru da yanzu haka yake buga wa kulob din Anzhi Makhachkala da ke Rasha kwallo, Samuel Eto’o ya bayyana aniyarsa ta komawa…

Samuel Eto’oShahararren dan kwallon Kamaru da yanzu haka yake buga wa kulob din Anzhi Makhachkala da ke Rasha kwallo, Samuel Eto’o ya bayyana aniyarsa ta komawa kulob din Chelsea da ke Ingila.
Eto’o dan kimanin shekara 32 ya ce mai yiwuwa ne ya canza sheka zuwa Ingila da zarar ya samu damar haka musamman ganin yadda kulob dinsa na yanzu yake fuskantar matsaloli.
Sai dai tuni kulob din Inter Milan da ke Italiya ya nuna sha’awarsa na dauke Eto’o musamman ganin daga kulob din ne dan kwallon ya canza sheka zuwa Rasha a shekarun baya.
A lokacin da Eto’o yake buga wa kulob din Inter Milan na Italiya kwallo a karkashin horarwar Jose Mourinho ne ya samu nasarar lashe kofin Serie A da na Coppa Italiya da Supercoppa Italiana da kuma kofin zakarun kulob-kulob na Nahiyar Turai (UEFA Champions League).
“Babu wani kocin da ya kai Jose Mourinho.  Na yi kwallo a karkashin kulawar  masu horarwa da dama amma ban ga wanda ya kama kafarsa ba”, inji Eto’o a lokacin da yake tattaunawa da jaridar Daily Mail.
“Yana daga cikin kococi masu hazaka da ake ji da su a duk fadin duniya kuma mun samu nasara tare da shi a kulob din Inter Milan don haka zan so mu sake hadewa da cigaba da wasa a karkashinsa”.
Ya zuwa shekaranjiya Laraba wani rahoto ya ce da wuya kulob din Anzhi ya kyale Eto’o ya bar kulob din  duk da matsalar kudi da yake fuskanta.  Kulob din ya sha alwashin biyan dan kwallon duk basussukan da yake bi nan da ba dadewa ba don hana shi canza sheka.