✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Watan Yaki da Ciwon Daji na Babban Hanji

Wannan wata na Maris da ya kama a yau hukumomin lafiya na duniya suka ware duk shekara domin fadakarwa a kan hanyoyin da za a…

Wannan wata na Maris da ya kama a yau hukumomin lafiya na duniya suka ware duk shekara domin fadakarwa a kan hanyoyin da za a bi a kiyaye ciwon daji na babban hanji. Shi ciwon daji na babban hanji kari ne da kan fito a can kasa-kasan babban hanji kuma a sannu sai ya girma ya yadu ya taba wasu sassan kayan ciki kamar karamin hanji. Yana da kyau a san cewa shi karamin hanji a karan-kansa da wuya ya samu karin da zai zama ciwon daji. Akan iya samu amma da wuya.

Ciwon ya fi kama manya wadanda shekarunsu suka haura 50, amma akan iya samu a wadanda shekarunsu ba su karasa 50 din ba da kadan. Ya fi kama maza fiye da mata. Abubuwan da suka fi jawo shi bayan yawan shekaru sun hada da rashin motsa jiki, kiba, yawan cin jan nama, kin cin kayan ganye da na ’ya’yan itatuwa, shan taba sigari da shan barasa.

Alamomin cutar sun hada da yawan taurin bayan gida a wadanda shekarunsu suka doshi 50 ko suka haura hakan, sai yawan yin bakin bayan gida (wanda ke nufin bayan gida mai jini ke nan) ko ma a ga ana yawan bayan gida da jini kamar mai basur. Sai yawan saurin gajiya idan ciwon ya dade a jiki. Akwai ma rama da rashin son cin abinci idan ciwon ya dade a jiki. Ba a cika wani samun ciwon ciki sosai ba, shi ya sa mutane da dama masu matsalar sai su dauka abin zai zo ya wuce, domin kusan bincike ya tabbatar idan da akwai ciwon ciki matsananci da ciwon ya fara nan da nan za a tafi a nemi magani.

Hanyoyin da akan bi a kiyaye wannan ciwo daga aukuwa ke nan sun hada da

1.        Rage yawan cin jan nama, a rika surkawa da farin nama (na kaji da na kifi da sauransu)

2.        Daina shan ruwan barasa (giya).

3.        Daina busa hayakin taba sigari

4. Yawan cin ganyaye da ’ya’yan itatuwa

5. Sai yawan cin kayan hatsi irin su masara, dawa, maiwa, gero da sauran abincin gargajiya musamman wadanda ba a surfa ba suna kiyaye wannan ciwo, shi ya sa da wuya a samu ciwon a tsakanin mutane kauye sai dai na birni

6. Yawan motsa jiki

7. Bincike ya nuna cewa yawan shan ruwa sosai a kullum zai iya rage hadarin kamuwa da ciwon

8.        Duk wanda ya kai shekara 50 in dai yana so ya kiyaye kansa daga wannan matsala akan ba shi shawara da ya rika zuwa awo duk bayan shekara biyu, wanda ake kira screening. A wannan gwaji akan gano farkon tsiron tun kafin ya zama daji ta hanyar duba bayan gida a dakin bincike a gani ko akwai kwayoyin halittun ciwon daji a ciki ko kuma ta hanyar haskawa da kyamara a duba ko akwai kari.

Binciken lafiyarmu domin kiyaye cututtuka ba wani abu mai wahala ba ne. Kawai mutumin da ya haura shekara 50 ya je  babban asibiti ya bude fayil ya ce yana so a rika yi masa binciken lafiya ne na daidai shekarunsa. Wato ke nan ba wai dole sai ana da wani ciwo ake ziyartar asibiti ba, a’a ana so a rika zuwa asibiti domin kiyaye cututtuka wato screening.

 

Ko shin akwai bambancin dorin gida da na asibiti idan mutum ya samu gocewar kashi ko ya karye?

Daga Aliyu B.D, Kaduna

 

Amsa: Akwai bambanci sosai ma kuwa. Ai idan ka lura a dorin gida yawanci mutum yana ihu yana jin zafi ake danne shi a yi dorin. Sa’annan duk da yake akwai wadanda suka nakalci dori a gargajiyance, amma dai wasu lokutan ba a samun dori ya hau daidai, sai mutum ya warke da gejeriyar kafa ko karkatacciyar kafa idan a kafa ne aka samu matsalar. Ba a cewa ba a samun gajarcewar kafa a na asibiti kwata-kwata, amma dai karkacewa da wahala. Wadansu masu dorin gargajiya a wannan zamani amma yanzu mun ga suna aikawa ana yin hoton D-ray domin su ga a ina takamaimai matsalar take kafin su yi dorin domin rage kura-kurai.

Duk wasu magunguna da za a bayar a asibiti masu amfani ne tun daga na kashe zogi da na kiyaye abubuwan da kan faru idan mutum ya samu irin wannan matsala. Ba za a iya tantance sahihancin na gargajiya a kimiyyance ba, idan ma an bayar ke nan.

Yawanci abin da ya sa mutane suka fi son na gida kawai saboda saukin kudi ne, domin aikin kashi da kwanciya a asibiti babban jidali ne ga aljihu. Da za a samar da kiwon lafiya kyauta ko mai rahusa sosai da za ka ga masu zuwa na asibitin sun fi masu zuwa wurin na gida yawa.

 

Ni kuma na ina duba mudubi ne sai na lura da wani abu a kwayar idona yalo-yalo kusa da dan bakin nan, amma ba na jin wani ciwo ko zafi ko matsalar gani. Ko shin wannan matsala ce?

Daga Jinjiri Musa, Kazaure

Amsa: Eh, ana samun wani tsiro a kan farin kwayar ido mai ruwan dorawa ko ruwan kasa, amma wanda ba ya da wani hadarin zama daji. Sai dai yana da hadarin hana gani sosai idan ya zo ya taba dan bakin nan. Wato zai iya girma ya hana gani kamar yadda yanar ido take yi. Za a gan shi kamar datti amma ko an wanke ido ba ya bacewa. Irin biyu ne a likitance akwai pinguecula akwai pterygium. Dukansu idan likitan ido ya duba ya gani zai iya tantancewa ko wanda dole sai an cire ne ko kuma ba sai an cire ba.