Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Wayar hannu ta cutar da masu sana’ar kaftani – Malam Tijjani

Malam Ahmad Tijjani Sulaiman

Malam Ahmad Tijjani Sulaiman ya kwashe shekara 25 yana sana’ar dinkin kaftani a Kasuwar Barci da ke Kaduna a Jihar Kaduna. A zantawarsa da Aminiya ya bayyana kalubalen da suke fuskanta a sana’ar  da kuma alheran da ya samu a cikinta:

 

ADVERTISEMENT

Aminiya: Shekaru nawa ke nan da ka fara wannan sana’a ta dinkin kaftani?

Na fara sana’ar dinkin kaftani kusan shekara 25 da suka wuce kuma shi ake yi har yanzu ba a daina ba.

ADVERTISEMENT

Aminiya: Ga dukkan alamu ka samu alheri da wannan sana’a ko?

Kwarai da gaske kuwa an samu alheri sai dai godiya.

Aminiya: Ko za ka fadi kadan daga cikin alheran da ka samu?

Yanzu haka kangona na nan a Unguwar Rigasa muna ta kokarin yadda za mu kammala domin a koma ciki tare da iyali. Kuma ta wannan fuska aka samu abin ginawa. Saboda haka mu kaftani babu abin da za mu ce da ita sai godiya.

Ta wannan gaba ne nake jan hankalin samari cewa koda sun yi karatu kada su yi wasa da sana’ar hannu. Saboda ita ce, za ka tashi ka je wani gari ba ka san kowa ba amma gari na wayewa da ka tambayi inda teloli suke za ka samu abinci.

Aminiya: A cikin wadannan shekaru da ka kwashe kana wannan sana’a wadanne garuruwa ka ziyarta?

Gaskiya na je garuruwa da dama amma ga misali a shekarun baya Jihar Kano muke kai kaya sai ta kai lokacin da abin ya bunkasa su ke zuwa nan sayen kayan. Muka koma muna zuwa Katsina, daga nan na koma Sakkwato. Amma yanzu saboda zamani ya zo da waya kawai za a kira sai a tura kaya jihohin da kake son a kai su. Su kuma ’yan kasuwa sai kawai su aiko da kudi.

Ba tare da kai ka bar Kaduna ba ko kuma shi mai sayen kayan ya baro Sakkwato ba. Sai dai kawai ka tura kaya ta mota a kai wa mai saye a Sakkwato. Kana zaune zai kira ka ya ce, na karbi kaya. Ba wani abu ya kawo haka ba sai rikon gaskiya da kuma jajircewa a kan sana’a.

Aminiya: Da wannan sana’a kake ciyar da iyalinka?

Kwarai kuwa, ni ke da iyali domin ’ya’yana 12 kuma da abin da ake ciyar da su ke nan ake kuma biyan kudin makaranta daidai gwargwado. Mun san Allah ke ciyarwa amma ta wannan hanya muke ci muke sha.

Aminiya: Ko za ka fada mana nau’in kaftanin da kuke yi a Kasuwar Barci?

Akwai kufta da kaftani da jere akwai siriya da kuma wadda ake kira rawar tila da sauransu.

Aminiya: Wane kalubale kuke fuskanta a wannan sana’a?

Kalubalen da muke fuskanta wanda har yanzu muna fuskanta shi ne da farko dai mun dauka ci gaba ne muka samu amma daga bisani kuma sai ya cutar da mu. Da farko dai na ce, mu ke zuwa garuruwa mu sayar da kaya kafin daga baya su ke zuwa saye a wajenmu har ta kai bayan wayar hannu ta shigo sai muka koma yin magana kawai sai a aika da kaya su kuma su aiko da kudi. To, wannan abu ya cutar da mu kuma duk mai sana’ar kaftani zai ce maka ya samu cutuwa da hakan.

A kwanakin baya idan suka zo rumfa-rumfa suke bi suna zabar kayan da za su biya ko saya idan ka iya aiki mai kyau har riga 10 sai a saya a hannunka a kuma biya ka. Idan an je wajen zaben riga biyu haka dai za a yi ta bi ana sayen riguna. Sai ya kasance wannan abu da ya fito da mu ganin kamar alheri ne sai ya cutar da mu domin za su aiko da kudi su fada ta waya cewa, a aika musu da kaya iri kaza da kaza. Idan aka tashi tura musu kaya sai a aika da wadanda inda su suka zo ba za su saya ba. Daga nan su ma sai suka rika buga waya ga wadanda ke aika musu da kaya cewa ko za su aiko da wasu kayan domin su sirka da wadanda ke hannunsu ko za su samu saiduwa.

Ashe wutar gada ce suka dora su a kai, to an saida ba a saida ba kai dai kana nan shi yana can ba za ka sani ba. A irin wannan a ’yan kasuwarmu ta Barci wadanda suka karye ba su kirguwa. Wannan shi ne kalubale na farko da ’yan kaftani ke fuskanta kuma suke ci gaba da fuskanta kuma kananan ’yan kaftani ke cutuwa fiye da manya. Su ma manyan na cutuwa saboda sai su tura kaya na Naira dubu 500 amma a shekara ko dubu 200 ba sa samu ba.

Aminiya: Ke nan wayar hannu a sana’arku ta cutar da ku?

Da farko dai mun dauke ta alheri ne a gare mu amma daga bisani ta cutar da mu. Saboda da ita aka yi amfani aka hana masu zuwa saye zuwa kasuwa da kansu sai dai a tura musu kuma sai aka rika tura musu kaya marasa kyau daga nan kuma su ma sai suka rika ramawa ta hanyar karbar bashi su ki biya.

Sai ya kasance su sun cutu mu ma mun cutu. Wannan abu har gobe shi ke cutar ’yan Kasuwar Barci.  Yanzu haka sai ka yi riga mai kyau ka ce za ka sayar, idan har ba faduwa za ka yi ba sai ka rasa mai saye.

Aminiya: Nawa ake sayar da riga a Kasuwar Barci yanzu?

A Kasuwar Barci dai zan ce, idan ka kai riga ba ta da wani tabbataccen farashi. Ba don komai ba akwai matasa da ba su da wani nauyi a kansu ma’ana idan yamma ta yi za su koma gida su ci abinci. Muna sararwa da masu zuwa saye a kan Naira dubu shida riga ko Naira 5,500 ko dubu 5. Amma yaro matashi da ba ya da wani nauyi a kansa idan ya zo da riga kana nuna mai babu kudi a hannunka sai ya karyar da rigar har Naira 3,500, shi dai bukatarsa kawai ya karbi kudi. Ya sayi yadi ya sayi zare da sauran duk abin da ake bukata wajen dinkin rigar amma ya karyar da ita. Babu ruwansa da wahalar da ya yi wajen yin aikin.

Aminiya: Wane jan hankali za ka yi ga matasan masu irin haka?

Kirana ga matasa su sani cewa koda ba su da wani nauyi a kansu su rika tunawa a kasuwar akwai babanninsu ko kakanninsu wadanda su da sana’ar suka dogara kuma da ita suke cin abinci. Ko ba su tausaya wa kansu ba to, su tausaya wa irin wadannan tsofaffi saboda su suna bakin cikin yadda koyaushe farashin ke kara lalacewa. Su sani suma nan gaba nauyin nan zai hau kansu idan kuma suka tausaywa su ma Allah zai kawo wadanda za su tausaya musu.

Aminiya: Ina mafita daga matsalar?

Abin da nake tattaunawa ke nan a kullum domin a samu mafita amma abin bai yiwu ba saboda rashin shugabanci. Komai na bukatar jagoranci kuma akwai bukatar a ce shugabanku mai hali ne idan a misali ka zo da rigarka daya kana son sayarwa saboda kila kana da wata ’yar matsala a gida ko rashin lafiya ko rashin abinci. Sai shugaban ya ce na san rigar nan kaza ce ga shi ma na saya je ka biya bukatarka. Wannan ne muka rasa.

Shi ya sa yau idan ka je da rigarka za ka sayar saboda rashin abinci ko kudi kana ji sai dai ka karyar da rigar ka yi hasara saboda ba mu da shugaban da zai iya dauke mana wannan nauyi.  Idan akwai shugaba doka za a kafa a ce duk wanda ya san ga yadda ake sayar da riga amma ya nemi karyata doka za ta yi halinta wajen hukunta shi.