✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wayyo Allah el-Rufa’i ka tausaya !!!

A ranar 29 ga watan Mayun da ta gabata ne aka rantsar da gwamnoni 29 da aka gudanar da zabe a jihohinsu kuma bayan an…

A ranar 29 ga watan Mayun da ta gabata ne aka rantsar da gwamnoni 29 da aka gudanar da zabe a jihohinsu kuma bayan an rantsar da su sun gabatar da jawabai ga jama’ar jihohinsu da nufin sanar da su muhimman abubuwan da suke da niyyar aiwatar wa domin inganta rayuwarsu.

A jihar Kaduna ma bayan an rantsar da Gwamna Nasir el-Rufa’i domin cigaba da mulkin jihar a karo na biyu ya gabatar da jawabinsa ga al’ummar jihar Kaduna.

A jawabin nasa ya bayyana irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu a wa’adin mulkinsa na farko, kamar inganta makarantun firamare guda dubu 4,200 tare da samar da tebura da kujeru domin magance zama a kasa da dalibai ke yi a yayin da suke daukar darasi.

Haka kuma gwamnatinsa ta mayar da ilimi kyauta kuma dole ga ‘ya’ya mata har zuwa matakin babban sakandare.

A bangaren lafiya kuma gwamnati ta yi kokarin inganta asibitocin jihar Kaduna da nufin samun cibiyoyin kula da lafiya a kusa da jama’a kuma ta mayar da kula da lafiyar yara kanana har zuwa shekara biyar kyauta a asibitocin gwamnati.

Gwamnan ya kuma tabbatar wa jama’ar jihar Kaduna cewa gwamnatinsa za ta cigaba da kokarin ganin ta hada kan al’ummar jihar da nufin kawo karshen rikicin kabilanci.

Haka kuma ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta tabbatar ta samar da ayyukan yi da kula da marasa lafiya da samar da ilimi ga kowai da kiyaye rayuka da dukiyoyin jama’ar jihar Kaduna.

Ya yi nuni da cewa, a wa’adin gwamnatinsa ta farko sun nuna karara cewa gwamnatinsu ta talakawa ce, kuma a yanzu  ma ba za ta yi watsi da su ba.

Gwamna el-Rufa’i ya yi dogon jawabi a wannan ranar da aka rantsar shi, inda ya yi bitar wadansu daga cikin ayyukan da gwamnatinsa ta gudanar da wadanda take da niyyar aiwatarwa a nan gaba.

Sai dai a karshen jawabin nasa sai ya fadi wata magana da ta girgiza al’umma kuma ya tsorata jama’ar jihar Kaduna, inda yake cewa: “kalubalen da ke gabanmu suna da yawa kuma masu tsauri ne, amma idan muka yi aikinmu yadda ya kamata za mu iya magance su tare da taimakonku da goyon bayanku da addu’o’inku. Za mu cigaba da daukar matakai masu tsauri, a wani lokacin kuma masu tsanani, don haka muna neman afuwarku.”

Wannan bayanin da el-Rufa’i ya yi a karshen jawabinsa ya girgiza al’ummar jihar Kaduna da sauran masu sauraronsa, shi ya sanya mafi yawan kafafen watsa labarai wannan bayanin ne suka fi yayatawa, inda suka bayar da rahoton cewa  Gwamna el-Rufa’i  ya bukaci al’ummar jahar Kaduna su gafarce shi domin zai dauki matakai masu tsanani.

Masu sharhi suna ganin kamata yayi el-Rufa’i  ya yi amfani da wannan lokacin na sake rantsar da shi a karo na biyu domin yi wa al’ummar jihar Kaduna albishir da cewa wannan karon  za su dara, saboda an ji jiki a baya a sakamakon wadansu matakai masu tsauri da aka dauka a wa’adin mulkinsa na farko, tun da talakawa sun daure sun sake zabensa a karo na biyu, ya nuna sun fahimci manufarsa kenan, watau sun yarda da matakan da ya dauka a baya domin amfaninsu ne, ba don munanawa ya yi ba, don haka shi kuma sai ya saka masu ta hanyar sassauta matakai masu tsauri da ya dauka a baya domin su samu sauki a halin yanzu, maimakon ya kara tsaurarawa a kan matakan da ya dauka masu tsauri a baya.

Mutane sun ji jiki kuma har yanzu suna jin jiki, dauriya kawai suke yi, amma duk wanda yake zaune tare da talakawa.ya san lallai suna fuskantar matsaloli iri-iri, shi ya sanya duk masallacin da mutane ke haduwa da yawa su yi sallah zai yi wahala a yi sallah ba a samu wani ya tashi yana neman taimako ba. A wannan karamar sallar da ta.gabata mutane har gida suke zuwa suna neman a ba su zakkar fid-da-kai, wanda hakan ya nuna cewa lallai ana cikin matsuwa, domin a baya suna zaune a gidajensu ake kai musu, amma bana masu bayarwar ma ta kansu suke yi, watau ruwa ya doki babban zakara ke nan.

‘Yan ta’adda sun takura mutane, sun hana talakawa zuwa gonakinsu, wadanda suka yi noman kuma an kama dan uwansu an yi garkuwa da shi an sanya masu kudin fansa, dole sun karyar da amfanin gonar da suke da shi tare da hadawa da wadansu kayayyakin suka sayar domin ceto dan uwansu, saboda haka an karya su, yanzu suna cikin halin kaka-ni-ka-yi.

Saboda haka don Allah mai girma Gwamna Nasir Ahmaf el-Rufa’i ka tausaya wa takalawan jihar Kaduna domin wallahi sun ji jiki kuma har yanzu suna jin jiki. Idan akwai wani mataki da aka san yana da tsauri da za a dauka to a yi kokari a yayyafa masa ruwa.yadda jama’a za su samu sauki.

A halin.yanzu kam mutanen jihar Kaduna cikinsu ya duri ruwa, suna tunanin mene ne kuma gwamna zai yi mai tsanani da har ya nemi gafararsu kafin ya aiwatar?  Zai kara rage ma’aikata ne, ko zai rage masarautu ne, ko zai cigaba da rushe-rushe ne? Jama’a dai a halin yanzu suna cikin zullumi, don haka el-Rufa’i ka tausaya masu, kada ka sanya wadanda ba su zabe ka ba su yi wa talakawan da suka fito kwansu da kwarkwatarsu suka zabe ka dariya. Domin wadansu na cewa wai ka yi lambo ne ka sassauta tsauraran matakan da kake dauka saboda kana so a sake zabenka,  bayan zabe za ka cigaba da daukar tsauraran matakai, don haka don Allah ka daure ka ba marada kunya.