✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wazirin sarkin musulmi na 12 ya rasu yana da shekara 85

A makon da ya gabata ne Allah Ya yi wa wazirin Sakkwato na 12, Alhaji Dokta Usman Junaidu rasuwa. Dokta Usman Junaidu ya rasu ne…

A makon da ya gabata ne Allah Ya yi wa wazirin Sakkwato na 12, Alhaji Dokta Usman Junaidu rasuwa.

Dokta Usman Junaidu ya rasu ne a ranar Allhamis da dare, sannan aka yi jana’izarsa  a Hubbaren Shehu danfodiyo a ranar Jumu’a bayan an masa sallah a masallacin Sarkin musulmi Bello.

Dokta Junaidu ya kwanta dama ne a gidansa da ke Unguwar Gidadawa a birnin Sakkwato bayan ya yi fama jinya na tsawon shekaru .

Marigayin ya rasu yana da shekaru 85, kuma shi ne Waziri na 12 bayan ya gaji mahaifinsa Waziri Juidu a shekarar 1997.

Margayi Usman malami ne, kuma masanin harkokin gwamnati, kuma ya yi karatunsa na digiri a jami’ar Al’azhar da ke kasar Masar in da ya karanci shari’a (shari’a Law). Sannan kuma malami ne kuma shugaba a Kwalejin ilmin Larabci da Musulunci(College of Isalmic Studies and Arabic) wadda ta koma kwalejin tunawa da Shaikh Abubakar Mahmud Gummi. 

Ya rike mukamai a matakin karamar hukuma da jiha har ya taba zama shugaban karamar Kebbi a lokacin da ba a kirkiri Jihar Kebbi. Bayan wadannan ayyukan ne ya karbi Wazirin Sarkin Musulmi, kujerar da yake kai fiye da shekara 21 har ya bar duniya.

Aminiya ta zanta da babban dan margayin, Farfesa Abdulkadir Usman Junaidu kan rayuwar mahaifinsu da mutanen jihar ke yabon saukin kansa da jajircewarsa wajen cimma bukatarsa na taimakon al’umma baki daya. Sai ya ce  “A yanzu ni ne babba a gidan kasancewa yayana Dokta Sanusi ya rasu kafin rasuwar Waziri. Mu 12 ne ke raye a yanzu maza biyar mata bakwai. Rayuwar margayi ba don yana mahaifina ba, duk mutumin dana gani irinsa ina girmama shi saboda tsare gaskiya, rikon amana da son zumunci da fadin gaskiya komai dacinta ga kowa a kowane lokaci. Duk wanda ya san shi zai fada maka cewa ya kasance malami wanda ya kama kansa ya mayar da kansa ga ubangiji. Abin duniya ba ya rudarsa. 

Baya da bukatar tara abin duniya, zumunta da hakkin Allah da iyalansa shi ne abin da ke gabansa, shirinka da Waziri ka tsaya ga gaskiyarka, za ku saba komai mukaminka.

“Da yawa akwai iyaye irin haka, bambancin da za ka gani tsakaninsa da su shi ne ya kasance mutum ne da ‘ya’yansa da na ‘yan uwa ke tsoron yin abin da ba daidai ba a gabansa don tsoron hukuncin da zai dauka. Ba ya wasa da aikata rashin daidai. Duk mai son su zauna lafiya sai ya yi koyi da irin halayensa.” In ji Farfesa Abdulkadir.

Farfesan ya kara da cewa sun koyi darussa da yawa wajen marigayin, inda ya ce  “Yana so a tsare hakkokin ubangiji matuka. Duk abin da ya sabawa shari’a ka guje shi kar ka zama rago, ka nemi na kanka ka bai wa ilmin Muhammadiya da Boko muhimmanci da rashin lalaci. A lokacin muna yara ya taba ajiye ni a makaratar da nake karatu da dare ba kowa cikin makarantar don al’adar yara ba sa komawa lokacin da hutu ya kare, haka ya barni ya dawowarsa a mota. Ba kowane uba ke yin haka ba, ka ga muhimmacin da ya ba karatu ke nan, wadannan ne darussan da muka koya a wurin Waziri” in ji Farfesa.

A game da gibin da ya bari kuwa, cewa ya yi “A duk lokacin da ka yi rashhin malami, to ka rasa gibi ba ka tunanin wani ya zo ya cika, sai dai a kwatanta. Ko yaushe ba a rasa masu ilmi, masana amma duk lokacin da ka rasa daya daga cikinsu, ka yi babban rashi. Sai dai Allah Ya gafarta musu.” Inji shi.

daya daga cikin daliban margayi Waziri Usman Junaid, Dokta Baba Sakkwato a zantawarsa da wakilinmu kan rayuwar Waziri ya ce “Malam ko da muke tasowa, mun same shi dattijon kansa ne mai iyali, Sardaunan Sakkwato ya kafa wata makaranta da ake kira Nizzamiyya Islamiyya, ‘yar Akija ya roki duk manyan sarakuna da malaman Sakkwato a basu yara don karantar da addini. 

Don haka ne aka tura Malam ya tafi can don koyar da yara karatu tun a 1957. A dilibansa da zan iya tunawa akwai ni, sai margayi Dokta Umar Bello da margayi Dokta Abubakar Muhammad Sakkwato na ‘yar Akija da ke jami’ar Usman Danfodiyo da Malam Abubakar Mahe darakta a ma’aikatar labarai da Al’adu da Malam Isah Attahir Kalfu da margayi Malam Abubakar Mai linzame ramen ige da Farfesa Habib Muhammad da  Farfesa Bello Sa’idu da sauransu.

“A matsayina na al’majirinsa da ya yi aiki tare da shi, kuma na san shi baya wasa da aiki. Yana kulawa da malamai da dalibai. Ya na da karfin hali kan tsaya kan gaskiya. Ko a majalisar sarkin Musulmi ya na fadin gaskiya komai dacinta domin shi ne Wazirin sarki, ka ga dole ya fada wa sarki gaskiya,” in ji shi.