✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wenger ya burge ’yan kallo a wasan sada zumunta

Tsohon kocin kulob din Arsenal da ke Ingila Arsene Wenger a ranar Litinin da ta gabata ne ya burge daruruwan ’yan kallo a wani wasan…

Tsohon kocin kulob din Arsenal da ke Ingila Arsene Wenger a ranar Litinin da ta gabata ne ya burge daruruwan ’yan kallo a wani wasan sada zumunta da kasar Faransa ta shiryawa tsofaffin ’yan wasanta.

Faransa dai ta shirya wasan ne ga tsofaffin ’yan kwallonta musamman wadanda suka lashe mata kofin kwallon kafa na duniya a 1998 kuma za ta yi amfani da kudin tikitin shiga wasan ne don tallafawa gajiyayyu da marasa galihu.

A yayin wasan, an ga yadda tsohon kocin Arsenal Wenger ya rika burge ’yan kallo wajen lailaya kwallo.  Akwai lokacin da ya yanki Zinedine Zidane da hakan ta sa ’yan kallo suka barke da ihu da sowa don murna.

Wenger duk da bai taba bugawa kulob din Faransa kwallo a rayuwarsa ba, ya yi wasa ne a wasu kananan kulob da ba su yi fice ba a Faransa kafin ya zama koci.

Rahotanni sun nuna kocin Real Madrid na yanzu Zidane ya yabawa Wenger a bisa kokarin da ya yi a lokacin wasan, kuma ya yi mamakin duk da irin tsufar Arsene Wenger ya nuna bajinta a lokacin wasan.

Daga cikin tsofaffin ’yan kwallon da suka amsa gayyatakuma suka buga wasan akwai Zinedine Zidane da Didier Deschamps da Fabien Barthez da Laurent Blanc da sauransu.

Tun bayan da Arsene Wenger ya bar kulob din Arsenal har yanzu bai fara horar da wani kulob ba.