Subscribe
 • facebook
 • twitter
 • whatsapp
 • linkedin
Wurare 18 da ke fuskantar barazanar dokar kulle a Najeriya

Wani yankin ‘Yan Kura da ke cikin Sabon Gari a jihar Kano a ranar Juma’a . Hoto Sani Maikatanga

Wurare 18 da ke fuskantar barazanar dokar kulle a Najeriya

Kananan hukumomi 18 a Najeriya na fuskantar barazanar dokar kulle kasancewarsu dauke da kaso 60 cikin 100 na masu COVID-19 a kasar.

Shugaban Kwamitin Yaki da annobar coronavirus na Fadar Shugaban Kasa Boss Mustapha, bayan gabatar wa Shugaba Buhari rahoton kwamitin a ranar Litinin 29 ga watam Yuni, ya nuna bukatar dokar kulle a kananan hukumomim domin dakile yaduwar cutar.

“Matakin kulle a kananan hukumomin 18 ba hurumin Gwamnatin Tarayya ba ne, hurumi ne na gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi”, inji shi.

Ko da yake Boss Mustapha bai ambaci sunayen kananan hukomomin ba, wani binciken da Aminiya ta yi na alkaluman da Hukumar Yaki  da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta fitar zuwa ranar sun jerin kananan hukumomi 20 da suka fi yawan masu cutar.

A cikin kananan hukumomin 20 jihar Legas na kan gaba da 11, inda karamar hukumar Lagos Mainland ke da kaso mafi yawa na masu cutar, su 1,274.

Ga jerin ragowar kananan  hukumomi 20 da suka fi yawan masu dauke da cutar coronavirus Najeriya da adadin masu cutar kamar yadda Aminiya ta binciko:

Jihar Legas

 • Lagos Mainland (1,274),
 • Mushin (458),
 • Eti-Osa (403),
 • Alimosho (239),
 • Kosofe (175),
 • Ikeja (168),
 • Oshodi/Isolo (132),
 • Apapa (131),
 • Amuwo Odofin (129),
 •  Lagos Island (111)
 • Surulere (110).

Babban Birnin Tarayya (Abuja)

 •  (AMAC (536).

Jihar Kano

 •  Tarauni (248),
 • Nassarawa (152).

Jihar Katsina

 • Katsina  (242).

Jihar Borno

 • Maiduguri (167).

Jihar Jigawa

 • Dutse (170).

Jihar Ondo

 • Oredo (126).

Jihar Bauchi

 • Bauchi (114).

Jihar Ogun

 • Ado Odo/Ota  (107).
Alkaluman NCDC na daren Litinin 30 ga watan Yuni, sun nuna cewa mutum 25,694 ne suka taba kamuwa da cutar coronavirus a Najeriya.
Mutum 9,746 daga cikinsu sun warke, 15,358 na nan suna jinyar cutar, yayin da mutum 590 suka rasuta dalilinta.